Yadda kungiyar ‘yan banga suka kashe makiyaya 11 a jihar Katsina

0

Kungiyar ‘yan banga dake karamar hukumar Kurfi sun kashe wasu makiyaya Fulani 11 a jihar Katsina bisa zargin hannu da suke da shi wajen kai wa mutanen yankin hari.

Yadda kungiyar ‘yan sa-kai suka kashe makiyaya 11 a jihar Katsina

‘Yan bangan sun cafke wadannan makiyaya ne a Wurma lokacin da suka shigo kasuwa yin cefani.

Wata majiya ta bayyana wa manema labarai cewa ‘yan bangan sun tsare wadannan makiyaya a Dutsin Karare kafin su kashe su.

Sai dai kuma mazauna yankunan sun koka kan kashe wadannan makiyaya da ‘yan bangan suka yi cewa hakan na sa yan uwan su su yi wa mutanen kauyukan diran mikiya su karkashe su da sunan ramuwar gayya.

Amma kuma wasu sun ce hakan da aka yi musu ya yi daidai domin sun addabi mutanen yankin babu kakkautawa.

A karshe kakakin rundunar’yan sandan jihar katsina Gambo Isah ya tabbatar da aukuwar haka yana mai cewa ‘yan bangan basu yi daidai ba kisan da suka aikata domin su ba hukuma bane.

Ya ce rundunar za ta gudanar da bincike akai kuma duk wadanda aka samu na da hannu a wannan kisa zai fuskanci hukuma. ” A dalilin irin haka ne yasa gwamnati ta rusa kungiyoyin ‘yan banga a ko’ina a fadin jihar.

Share.

game da Author