Yadda jami’an ilmi su ka nemi rufe bakin shugabannin sakandaren Barno daga sanar da Zulum tabarbarwar karatu a jihar

0

Gwamna Babagana Gana Zulum na Jihar Barno, ya ce manyan jami’an Ma’aikatar Ilmin Jihar Barno sun yi wa Shugabannin Sakandaren Jihar barazanar cewa kada su kuskura su shaida wa Zulum munin tabarbarewar da ilmi ya yi a jihar.

Zulum ya ce jami’an sun yi wa ‘principals’ barazanar cewa duk wanda ya sanar da gwamna halin da ilmi ke ciki a jihar, to za su cire masa mukami, sannan su canja shi.

Zulum ya ce sau da yawa ya sha zagayen gani da ido a makarantu, amma ko ya tambayi matsaloli da kalubalen da ake fuskanta, shugabannin sakandaren ba su fada masa.

Gwamna Zulum ya yi wannan kakkausan bayani a Maiduguri, lokacin da ya ke taron keke-da-keke da shugabannin sakandaren gwamnatin jiha na Barno su 84.

Zulum ya yi wannan ganawar kai tsaye da su ne domin gano gaskiyar lamarin halin tabarbarewar da ilmi ya yi a jihar.

An yi ganawar yayin da dalibai su ka koma makaranta, watanni bakwai bayan barkewar cutar korona.

Daga nan Zulum ya roke su cewa, “don Allah ku shaida min gaskiyar halin da ilmi ke ciki, domin a yi gyara. Na yi maku alkawarin cewa babu abin da zai same ku.”

Duk da haka sun ji tsoro, domin a cewar su, akwai munafikan da za su fita su bayyana sunayen wadanda su ka gaya wa Gwamna gaskiya.

A kan haka ne ya ce ya ba su mako daya kowa ya kawo dalilan a rubuce, ya ba shi hannu da hannu.

Duk da haka sun bada shawara da daina daukar ‘yan JSS1 daga firamare, kai tsaye ba tare da yin jarabawa ba.

Kuma a daina shiga SS1 ba tare da cin jarabawa ba.

Nan take Zulum ya amince da haka, kuma ya bada wannan umarnin.

Tun da farko Zulum ya nemi jin dalilin da ya sa daliban Barno da su ka kammala sakandare ba su iya shiga jami’a.

“Ko sun shiga ma, to ba gane darussan da ake koyarwa su ke yi ba.” Inji Zulum.

Share.

game da Author