Yadda jama’a su ka fasa rumbun ajiyar kayan tallafin korona, su ka yi masa ƙarkaf a Legas

0

Tirmitsitsi ya barke a Lagos, yayin da cincirindon mutane su ka fasa wani sito da aka ajiye kayan tallafin korona su ka rika jidar kayan abinci, a Monkey Village da ke Maza-maza, cikin unguwar Odofin.

Kayayyakin da aka rika jida din dai duk an buga masu tambarin ‘COCAVID’, NOT FOR SALE; wato kayan tallafin korona ne, ba na sayarwa ba ne.

Kayayyakin sun hada da shinkafa, macaroni, taliya, gishir, garri, sukari da kuma katan-katan na indomi.

Wani mazaunin unguwar ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa tun safe mazauna unguwar ke ta jidar kayan abincin.

“Da farko dai wasu mutane ne su ka isa sito din da safe su ka dauki wasu kayayyakin abincin. Dama sun saba zuwa kowane lokaci su na kwasa.” Haka wani mazaunin unguwar wanda ya roki kada a bayyana sunan sa, ya shaida wa PREMIUM TIMES.

“Lokacin da mutanen su ka lodi kayan abinci za su tafi, sai aka rika rokon su su bai wa wadanda ke wurin, amma su ka ki. Bayan sun tafi sai aka taru aka fasa sito din, kowa ya rika jida kawai. Gwamnati ta kimshe abinci, ba ta raba ba, ga kuma jama’a na cikin halin kunci.”

Share.

game da Author