Yadda aka yi ‘kwasar ganimar’ kayan gida na, duk da kyautatawar da na ke wa mazauna unguwar –Yakubu Dogara

0

Tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara, ya bayyana yadda masu tarzomar ‘kwasar ganima’ su ka kutsa cikin gidan sa suka yashe shi, a unguwar da wani gidan sa ya ke a Jos, duk kuwa da kyautatawar da ya ce ya na yi wa mazauna unguwar.

Matasa sun kutsa gidan ne a ci gaba da kwasar kayayyaki da su ka rika yi, bayan karshen zanga-zangar #EndSARS.

Gidan dai ya na cikin wata unguwa ce da ake kira Lamingo, a Jos. Ya ce abin ya ba shi haushi, ganin irin rashin mutun cin da mazauna yankin su ka yi masa, duk kuwa da cewa ya na rika kyautata masu bakin yadda zai iya yi a baya.

Dogara wanda kwanan baya ya canje sheka ya koma APC, ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa, “Abin da ya faru da ni, abin takaici ne. Saboda ban taba tunanin za a yi min irin wannan cin mutunci da rashin kyautawa a Jos ba.

“Jos ta zama kamar gari nan a biyu, banda garin da aka haife ni. Na shafe lokutan rayuwa ta mai yawa a Lamingo. Makwauta na a Lamingo da yawan su ina da kwakkwaran kusanci da su. Kusanci mai karfi.” Inji Dogara.

“Kun ga irin tsiyar mutanen ko? A baya na raba Keke Napep kamar 100 cikin Lamingo. Kwanan nan nayi wannan rabon a lokacin shagulgulan sallah. Kuma na yi niyyar sake yin haka idan bukukuwan Kirsimeti ya zo.

“Na rika sayen kayayyakin da aka kwashe ina tarawa domin rabawa, a duk lokacin da ga ina da sararinn wasu kudi a hannu na, to na yi rabawa a wata rana haka ta musamman,.”

Yakubu ya ce Keke Napep kusan 100 da ya raba, ta hannun mai’unguwar Lamingo ya damka rabon.

Ya ce ran sa ya baci matuka, ganin yadda ya raba masu kayan alheri ga jama’ar yankin a baya, amma hakan bai hana sun yi wa gidan sa karkaf ba.

“Na yi mamakin ganin yadda su ke kwashe komai na gidan, sai wasu ƴan tarkacen kayan harkokin yawon bude ido da wasu ƴan ma’adinai kadai aka bari.

An kai farmakin fasa wurare da dama a Jos, babban birnin Jihar Filato. Baya ga mutum 300 da sojoji su ka kama, an kara kama wasu da tuni an maka su kotu, an ci su tara.

Share.

game da Author