Tsohon Shugaban Hukumar Kare Hakkin Jama’a ya sha kaye a shari’ar sa da El-Rufai

0

Tsohon Shugaban Hukumar Kare Ƴancin Jama’a, Chidi Odinkalu, ya sha kaye a shari’ar da ya fafata da Gwamnatin Jihar Kaduna.

Mai Shari’a Peter Making na Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna, ya kori karar a ranar Alhamis, kuma ya rankwala masa tarar biyar naira 5,000 ga kowane wadanda ya maka kotu, ladar bata masu lokaci da ya yi.

Wadanda zai biya naira 5,000 din su hudu, zai biya naira 20,000 kenan.

Odinkalu, wanda fitaccen lauya ne, an bayyana a shafin Twitter na Ballason Gloria Mabeiam cewa hakan zai biya.

Sai dai kuma Gwamnatin Jihar Kaduna cewa ta yi naira 500,000 ce zai biya kowane wanda ya maka kara.

Tunda mutum hudu ya maka kotu, Odinkalu zai biya su ladar bata masu lokacin zirga-zirga kotu har naira milyan biyu kenan.

Sauran wadanda ya maka kotu sun hada da Daraktan Shigar da Kararraki na Jihar Kaduna; Kwamishinan ‘Yan Sanda na Kaduna; sai Sufeto Janar na Ƴan Sandan Najeriya.

Mabeiam wanda ta ce Odinkalu zai ɗaukaka kara an Kasa samun ta domin jin ta bakin ta.

Shari’a ta samo asali ne tun a cikin Fabrairun 2019 da Odinkalu ya yi bayani kai-tsaye a gidan talbijin, dangane da kashe kashen da aka yi a Kajuru, jihar Kaduna.

Ya karyata Gwamna Nasir E-Rufai inda ya ce ya samu rahoton adadin wadanda aka kashe.

Odinkalu ya ce majiyar sa ta shaida masa cewa ba a yi kashe-kashe ba a yankin.

Sai ya zargi El-Rufai da ƙirƙiro ƙarya domin ya ci ribar zabe a yankin.

A kan haka ne a cikin Maris, 2019, Gwamnatin Kaduna ta garzaya Kotun Majistare ta nemi a maka wa Odinkalu sammace.

Ta zarge shi da kokarin kitsa labarin ƙarya a talbijin da nufin haddasa fitina a Kaduna.

Odinkalu ya yi kokarin kotu ta kori karar, Amma bai yi nasara ba.

Sannan kuma bai yi nasara ba a kokarin da na maido shari’ar a Kotun Abuja.

Share.

game da Author