TSANANIN KISHI: Yadda uwa ta kashe ƴaƴan ta biyu saboda mijinta ya kara aure a Kano

0

Saboda tsananin kishi wata mata mai suna Hawwa dake unguwar Sagagi dake rukunin gidaje na Discos, dake Kano.

Shugaban Al’umma Ahmed Bello, ya shaida wa mutanen unguwan cewa Hawwa ta aikata wannan mummunar abu ne a lokacin da mijin ke gidan Amaryarsa.

Sannan kuma bayan ta aikata hakan sai ta fita da gudun tsiya. Rahotanni sun nuna cewa ko da makwabta suka yi kokarin kama ta, ta nemi ta illata wadanda suka tsaya a gabanta.

Kawun wadannan yara da ta kashe, ya bayyana wa ƴan sanda cewa tunda mahaifin yaran ya ƙara mata suke zaman lafiya ya ƙare a wannan gida, bala’in yau dabam da na gobe bam.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce zata cigaba da bincike akai.

Share.

game da Author