Ƙaramin Ministan Fetur, Timipre Sylva ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta samar da wuraren maida motocin ƴan Najeriya masu shan fetur, zuwa masu shan gas.
Sylva ya yi wannan jawabin a lokacin da ya kai ziyasa garejin da ake aikin maida motocin Gwamnati masu shan gas daga amfani da fetur din da su ke yi.
Ya ce tsadar fetur ce ta za a maida motocin Gwamnatin Tarayya zuwa masu amfani da gas.
Ya ce tuni an karkata motocin Fadar Shugaban Kasa da na ministoci da dama zuwa aiki da gas, maimakon aiki da fetur din da su ke yi.
Da ya ke jawabi lokacin da ya kai ziyarar ganin yadda aikin ke gudana a Garejin Aikin Maida Motocin Fetur Zuwa Gas a Jahi da kuma Garejin Autolady da ke Abuja, Karamin Ministan Fetur ya ce su ma ‘yan Najeriya za a samar da inda za a rika maida musu zuwa gas a wadace, kuma a saukake.
Ya kai ziyarar ce tare da Babban Sakataren Hukumar Ƙayyade Farashin Litar Man Fetur, Abdulkadir Saidu.
Gwamnatin Buhari ta janye tallafin man fetur, wanda hakan ya haddasa karin farashin litar fetur zuwa naira 161.
Asalin Matsalar Tsadar Fetur:
PREMIUM TIMES ta buga yadda Shugaban NNPC ya jaddada goyon bayan ƙarin Kuɗin fetur.
Shugaban Hukumar NNPC Mele Kyari ya sake jaddada goyon bayan cire tallafin fetur, wanda hakan ne musabbabin karin kudin fetur.
Ya ce an cire tallafin ne saboda shekaru da mada bayar da tallafin mai ya zama hanyar kashe makudan kudaden gwamnati a hanyar da ba ta da amfani.
Kyari ya yi wannan bayani a taron Kungiyar Masu Tace Danyen Mai na Afrika.
Hukumar NEITI ta tabbatar da cewa tsakanin 2009 zuwa 2011, Najeriya ta biya sama da naira tiriliyan 3 da sunan kudin tallafin mai.
Tallafin Talauta Najeriya:
Ƙuɗaɗen da ake biyan manyan dillalan fetur a matsayin kudin tallafi sun karu da kashi 71% a 2010.
Yayin da a 2009 gwamnatin Jonathan ta biya tallafin naira bilyan 406, a cikin 2010 ta biya naira bilyan 695.
Cikin 2011 kuma kuɗin sun karu da kashi 174%, inda aka biya naira tiriliyan 1.9 a matsayin kudin tallafin mai.
Ofsihin Akanta Janar ya ce an biya naira tiriliyan 2.83 kudin tallafin a 2009 zuwa 2011. Amma kuma Hukumar PPPRA cewa ta yi kudin sun zarce haka, naira tiriliyan 3.002 ce aka biya dillalan fetur da NNPC kudin tallafin.
Wato an rasa ya aka samu bambancin naira bilyan 175.9 kenan.
A karkashin mulkin Buhari, kuɗaɗen tallafin mai sun karu da kashi 210% a cikin 2018, inda aka rika biyan naira milyan 722.3 a kullum a cikin watan Maris.
Ƙuɗaɗen sun karu cikin watan Mayu, 2018 inda aka rika biyan naira bilyan biyu a kullum, a cikin watan Mayu.
Hakan ya ƙara kassara aljihun gwamnati ta yadda tilas Najeriya ta rasa mafita, sai ta fara fagamniya da gaganiyar ciwo dimbin bashin da har yau ba san ranar dainawa ba.