TATTALIN ARZIKI: Akwai alamun wahala nan gaba – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa shi irin rimtsin da tattalin arziki ya shiga sanadin ɓarkewar cutar korona, ya nuna cewa nan gaba za a ya shiga wani sabon halin ƙuncin tattalin arziki har zuwa shekaru huɗu.

Buhari ya yi wannan bayani a lokacin da ya ke gabatar da Kasafin 2021 a Zauren Majalisar Tarayya, ranar Alhamis a Abuja.

Ya gabatar da kasafin naira tiriliyan 13.08. Kasafin dai an yi shi a kan kowace dala ta na daidai da naira 376.

Sannan kuma an yi kasafin a kan gangar danyen man fetur dala 40. Kuma a cikin 2021 za a rika hako ganga milyan 1.86 a kowace rana.

Cikin jawabin, Buhari ya nuna Najeriya ba ta da kudin da za a kashe wajen aiwatar da kasafin, tilas sai an ciwo bashin naira tiriliyan 4.86.

Ya ce tattalin arzikin Najeriya ya fuskanci matsanancin kalubale, kuma kananan masana’antu da kananan hada-hadar kasuwanci duk wasu sun durkushe, wasu kuma sun gurgunce, saboda annobar korona.

Ya kara jaddada kudirin gwamnatin sa na kokarin ganin ta samar wa mutum milyan 100 aiki cikin shekaru 10.

Buhari ya gabatar da kasafin a daidai lokacin da kayan abinci da na masarufi ke tsada, har ta kai ga ma’aikatan Kungiyar Kwadago sun yi barazanar yin yajin aiki na game-gari, saboda karin kudin wutar lantarki da na fetur.

Cikin watan Agusta
Najeriya ta shiga halin matsin tattalin arziki wanda rabon kasar da shiga irin sa tun shekaru goma da su ka gabata. Haka dai Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS) ta tabbatar.

Share.

game da Author