Tarzomar #EndSARS ta ci rayukan ƴan sanda 22, aka ragargaza ofishin su 205 –Sufeto Janar

0

Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Muhammad Adamu, ya bayyana cewa an kashe jami’an ‘yan sanda 22 yayin da aka ragargaza ofisoshin su 205 a lokacin mummunar tarzomar #EndSARS.

Wannan tarzoma dai ta fara ne daga zanga-zangar lumana, tsawon makonni biyu, amma daga baya batagari su ka kwace ragamar ta, su ka rika kashe jami’an tsaro, kona ofisoshin su, banka wa kadarorin gwamnati da na jama’a wuta, sai kuma a karshe ta koma kwasar kayan tattafin korona, zuwa kwasar kayan manyan ‘yan siyasa.

Kafin nan dama sai da batagari da jami’an ‘yan sanda su ka rika kai wa masu zanga-zangar lumana farmaki a birane da dama, ciki har da Lagos da Abuja.

Yayin da ake gudanar da wata zanga-zanga ta lumana a Legas, sojoji sun bude wuta a sansanin da masu zanga-zangar su ka yi dafifi, abin da wadanda su ka shaida cewa sun kashe mutane da dama a wurin.

Sai dai kuma sojoji sun karyata labarin cewa sun bude wuta a wurin. Wannan ya haifar da hatsaniya har matasa su ka bazama daukar doka a hannun su.

Sojoji sun musanta bude wuta, amma sun tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Lagos ta gayyace su domin su tabbatar da doka da oda a kan titina.

Ita ma gwamnatin Legas ta ce ba ta gayyace sojoji su bude wuta a wurin masu zanga-zanga a Lekki da ke Lagos ba.
Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Duniya, Amnesty International, ta ce akalla an kashe mutum 56 sanadiyyar zanga-zangar #EndSARS a fadin kasar nan.

Shi kuwa Kakakin Yada Labarai na ’Yan Sanda, Frank Mba, cewa ya yi jami’an su sun gudanar da aikin su a cikin kwarewa a lokacin zanga-zanagar har karshen ta.

“Sufeto Janar ya jaddada cewa lokacin da zanga-zanga ta barke, aikin jami’an sa shi ne tabbatar da an bi doka da oda. Sun rika tsayawa gefen masu zanga-zanga da kuma kafada da kafada da su, idan sun a tafiya.

“Ko lokacin da zanga-zangar ta rikide zuwa tarzoma a wasu jihohi, jami’an tsaro bas u yi amfani da karfin ikon su ko karfin makaman su sun tankwara masu zanga-zanga ba.

“Rahotanni tabbatattu, kuma bayyanannu sun nuna an kashe jami’an ‘yan sanda 22, kuma duk kisan gilla aka yi masu. An kuma ji wa da daman su raunuka. A yanzu haka wasu na asibiti mutu-kwakai-rai-kwakwai.”

“Masu zanga-zanga sun ragargaza ofishin jami’an ‘yan sanda 205, masu yawa daga cikin su ma wuta aka banka masu, bayan an kwashe kayayyakin da ke ciki. An kuma saci kayan gwamnati da na jama’a, an lalata kadarori masu tarin yawa. Amma duk da haka jami’an mu ba su yi amfani da karfi wajen murkushe masu zanga-zanga ba.” Inji Adamu.

Share.

game da Author