Kwamitin Majalisar Dattawa ya ragargaji Ministan Harkokin Makamashi, bayan da kwamitin ya bankado yadda Ministan ya zabga ayyukan wutar lantarkin karkara a garuruwa 20 cikin Karamar Hukumar Lau, ta Jihar Taraba, inda can ne mahaifar sa.
Abin da ya fi bata masu rai, shi ne yadda Ministan zai yi nemi iznin samar da harken lantarki a garuruwa 20 a karamar hukumar sa, amma gaba dayan jihohin Kudu maso Kudu, a wuri daya kacal za a yi aikin samar da hasken lantarki a karkara, shi ne a Jihar Delta kawai.
Sanatocin sun yi wannan fallasa ce a ranar Laraba, lokacin da Shugaban Hukumar Samar da Hasken Lantarki a Karkara (Rural Electricity Agency), Ahmed Salijo ya bayyana gaban kwamitin domin kare kasafin hukumar na 2021.
Sanata Yusuf Yusuf ne ya fara fallasa yadda aka cusa ayyuka har 20 a garuruwa daban-daban cikin Karamar Hukumar Lau, mahaifar ministan, alhali a wasu jihohin ko turken fal-waya hukumar ba za ta kafa ko da a kauye daya ba.
“Kai jama’a! Da Ni na dauka aiki daya ne kadai Ministan Makamashi ya kai Karamar Hukumar Lau. To ku duba da idon basira a tsanake, za ku ga ayyuka 20 cif ya kai saboda can ne mahaifar sa.
“Kun gani ko! Ga wani aikin na naira milyan 52, ga wani na naira milyan 30, ga na naira milyan 20, ga kuma na milyan 40. Kai ga su nan dai birjik.
“Na tabbata kuma duk ya kai ayyukan ne, saboda Karamar Hukumar Lau can ne mahaifar sa.” Inji Sanata Yusuf.
Wasu Sanatocin kuma da aka ambaci wasu ayyukan da aka ce ana kan yi a yankunan su, sun ce kawai aikin duk a kan takarda ya ke. Saboda ba su san inda ake yi ba, kuma ba su ma san ‘yan kwangilar da aka ba ayyukan ba.
Sanata Bala Na’Allah, ya ce a gaskiya Ministan Makamashi ya karya rantsuwar da ya yi a lokacin da aka nada shi Minista.
“Don me zai fifita garin su wajen kai ayyuka fiye da ko’ina a Najeriya. Hakan na nuna cewa ba zai iya yin adalci ba kenan. Wannan kuma raunin jagoranci ne karara.” Inji Sanata Na’Allah.
A karshe dai Sanatocin sun shaida wa Shugaban Hukumar REA, Ahmed Salijo cewa idan ya fita, ya sanar da Ministan ya cewa sun bankado abin da ya turbude a cikin kasafin 2021, kuma ba abin da su ko sauran ‘yan Najeriya za su amince wa ba ne.
Discussion about this post