Sojojin saman Najeriya sun yi wa maɓoyar Mahara a dazukan Kaduna da Zamfara luguden wuta

0

Babban Hafsan Sojojin Najeriya Sadique Abubakar ya bayyana cewa yanzu fa maharan da ke addabar mutane a yankin Kaduna, Zamfara, Katsina da Neja sun kade.

Sadique ya bayyana cewa dakarun su baza su yi kasakasa ba wajen cigaba da yi wa mahara luguden wuta babu kakkautawa har sai sun fatattake su kaf a dazukan da ke kewaye da jihohin.

” Muna farinciki da gwamnatocin Kaduna, Katsina da Zamfara bisa irin bayanan da suke bamu da hadin kai da suke bamu.

” Mahara sun kade yanzu, basu da inda zasu biye yanzu, sai munga karshen kaf. Ba za mu kakkauta ba wajen yi musu luguden wuta daga sama. Wannan shine za mu ci gaba da yi kuma su sani duk inda suka tafi zamu bisu mu gama da su.

” Za mu tabbata duk wani maboyar su dake wannan yanki na Kaduna da Zamfara, munngama da shi.

Bayan haka Sadique ya gargadi ƴan ta’addan da ake cewa wai za su kafa sansanonin Boko Haram, ISWAP a yankin cewa su kwana da shiri domin soji ba za su bar su su yi motsi ba a duk inda ma suke a kasar nan.

” Za mu rika musu balbalin wuta daga sama, suku abokan aikin mu daga kasa su a bi sun bibbigewa, sannan kuma wadanda ke cikin al’umma, ƴan sanda su rika tsamo su daya bayan daya.

Sannan kuma ya yaba yadda ya ga matasan sojoji ƴan shekara 20 zuwa 30 na sarrafa manyan jiragen yake harda irin C130,yana mai cewa a shekarun baya sai soja da kai mukamin Birgediya Janar ne zai iya tuka irin waɗannan jirage.

Share.

game da Author