Shugaban Hukumar NNPC Mele Kyari ya sake jaddada goyon bayan cire tallafin fetur, wanda hakan ne musabbabin ƙarin kuɗin fetur.
Ya ce an cire tallafin ne saboda shekaru da mada bayar da tallafin mai ya zama hanyar kashe makudan kudaden gwamnati a hanyar da ba ta da amfani.
Kyari ya yi wannan bayani a taron Kungiyar Masu Tace Danyen Mai na Afrika.
Hukumar NEITI ta tabbatar da cewa tsakanin 2009 zuwa 2011, Najeriya ta biya sama da naira tiriliyan 3 da sunan kudin tallafin mai.
Tallafin Talauta Najeriya:
Kudaden da ake biyan manyan dillalan fetur a matsayin kudin tallafi sun karu da kashi 71% a 2010.
Yayin da a 2009 gwamnatin Jonathan ta biya tallafin naira bilyan 406, a cikin 2010 ta biya naira bilyan 695.
Cikin 2011 kuma kudin sun karu da kashi 174%, inda aka biya naira tiriliyan 1.9 a matsayin kudin tallafin mai.
Ofsihin Akanta Janar ya ce an biya naira tiriliyan 2.83 kudin tallafin a 2009 zuwa 2011. Amma kuma Hukumar PPPRA cewa ta yi kudin sun zarce haka, naira tiriliyan 3.002 ce aka biya dillalan fetur da NNPC kudin tallafin.
Wato an rasa ya aka samu bambancin naira bilyan 175.9 kenan.
A karkashin mulkin Buhari, kudaden tallafin mai sun karu da kashi 210% a cikin 2018, inda aka rika biyan naira milyan 722.3 a kullum a cikin watan Maris.
Kudaden sun karu cikin watan Mayu, 2018 inda aka rika biyan naira bilyan biyu a kullum, a cikin watan Mayu.
Hakan ya kara kassara aljihun gwamnati ta yadda tilas Najeriya ta rasa mafita, sai ta fara fagamniya da gaganiyar ciwo dimbin bashin da har yau ba san ranar dainawa ba.