SHEKARU 60 BAYAN ‘YANCI: Najeriya Ta Nausa Cikin Surkukin Dajin Da Babu Tabbacin Mafita

0

Ranar Lahadi a Babban Cocin Najeriya, wanda ba shi da nisa daga Babban Masallacin Najeriya da ke Abuja, Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, ya fito karara ya fadi mawuyacin halin da Najeriya ta shiga.

Har cewa ya yi, “bangon da Najeriya ta jingina da shi a tsatstsage ya ke, kuma idan ba da gaske aka yi ba, to zubewa kasa zai yi baki daya.”

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ne ya wakilci Osinbajo, a cocin domin yi wa Najeriya addu’o’in zaman lafiya da dorewa a matsayin dunkulalliyar kasa, daidai lokacin da ta ke cika shekaru 60 cif bayan samun ‘yanci daga hannun Turawan mulkin mallaka na Ingila.

Osinbajo kamar ya nanata abin da Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo ya furta ne makonnin da su ka gabata.

“Najeriya sannu a hankali sai kara zama ta ke yi kasar da ta lalace, ta na kara rabuwa, kawunan ‘yan kasar na rarrabuwa, sannan kuma ta na kara kasancewa cibiyar yunwa, talauci, fatara da kuncin rayuwa a duniya.” Haka Obasanjo ya ce.

Sai dai kuma kalaman Obasanjo ba su yi wa Fadar Shugaban Kasa dadi ba, domin Kakakin Yada Labarai na Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu, ya maida wa Obasanjo raddi cewa shi ne ‘Babban-Kwamandan-Raba-Kan Jama’a a kasar nan.

NAJERIYA: Babbar Kasa Ko Tubalin Toka?

Tun Najeriya ba ta wuce shekaru biyar da samun ‘yanci ba, ta fara afkawa kwazazzabon da har yau ta kasa fitowa, kuma an rasa mai karfin shiga ya ciccibo ta, ya fitar da ita.

Rarrabuwar kawunan da ke a zukatan al’ummar kasa, sannan da kuma rashin kishin ita kan ta kasar, ya sa an kasa hada kai domin a yi gangamin shiga cikin kwazazzabo a yi wa Najeriya daukar-daki, a ceto ta.

Juyin mulkin da ake gani na kabilanci ne, na 1966 da kuma yunkurin juyin mulki na 1967, su ne itace, kirare da makamashin da su ka fara ruruta wutar damalmalewar al’amurra a Najeriya.

Sai kuma shekaru biyu da rabi da aka shafe ana Yakin Basasa, shi ma ya kara maida Najeriya baya.

Fadi-tashin yawan juyin mulkin sojoji da aka rika yi tun daga 1966 har zuwa karshen mulkin su a 1999, shi ma wani gagarimin koma-baya ne ga Najeriya.

Soke zaben 1993, mutuwar dan takarar da ya yi nasara, marigayi MKO Abiola da kuma kisan matar sa, Kudirat da aka yi wa kisan-gilla, shi ma ya kara tauye Najeriya a wuri daya, kuma ya kara mayar da ita baya.

Duk da cewa Najeriya ta samar da hamshakan mutane ‘yan kishin kasa, to kuma ta kyankyashe tantiran baragurmin barayin gwamnati, wadanda su ka yi kaurin suna wajen wawurar dukiyar kasa.

Kadan daga cikin su akwai irin su James Ibori wanda ya yi gwamna a Jihar Delta. An daure shi a Ingila, ga kuma marigayi tsohon shugaban kasa na mulkin soja, wanda gwamnatin sa ta yi kaurin suna a duniya wajen mulkin kama-karya da karya masu adawa ana garkame su a kurkuku. Wasu ma, ciki har da marigayi Shehu ‘Yar’Adua, a kurkukun su ka mutu.

NAJERIYA: Dandalin Dandazon Barayin Gwamnati:

Har muhawara ake yi, ana cewa an rasa lokacin da aka yi satar kudin Najeriya. Shin a lokacin mulkin soja ne, ko kuwa a zamanin mulkin farar hula.

Kudaden da Abacha ya wawura, an rasa gane hakikanin adadin su. Har ma zalayar jama’a ake yi, an maida satar kudin da Abacha ya yi a matsayin barkwanci. Ana cewa ‘shi kadai ne ya mutu amma har yau bai daina aiko wa ‘yan Najeriya kudi daga lahira ba’!

Ana yin wannan zolayar ganin yadda har yanzu kasashen Turai da Amurka ba su gama maido wa Najeriya makudan kudaden da aka kimshe a can a zamanin Abacha ba, shekaru 22 bayan mutuwar sa.

Tsohuwar Mataimakiyar Shugaban Bankin Duniya, Oby Ezekwesili ta yi furuci tun cikin 2012 cewa barayin gwamnati sun saci kudi sun boye daga samun ‘yanci zuwa 2012, za su kai dala bilyan 400.

Ta kara cewa a duk shekara ana sace akalla kashi 20% bisa 100% na kasafin kudaden manyan ayyukan gwamnatin tarayya.

NAJERIYA: Attajirin Da Yunwa, Fatara Da Talauci Su Ka Yi Wa Katutu

Duk da dimbin arzikin man fetur, sannan da yawan al’umma da kuma harkokin kasuwancin da ke samar wa gwamnati kudaden shiga na ribar fetur da haraji, har yau kasar ba ta fita daga cikin jerin matalautan kasashen da yunwa, fatara da talauci su ka yi kaka-gida a gidajen sama da mutum milyan 100 a kasar ba.

Wasu kididdigar da cibiyoyi da kungiyoyi na Turai da na cikin gida su ka yi, sun nuna cewa akwai tsakanin mutum milyan 45 zuwa milyan 70, wadanda ba su da cin yau ko na gobe, har tilas a kullum sai sun fita sun nema.

Allah kadai ya san yawan mutanen da ba su iya samun kwatankwacin dalar Amurka 1 tal a rana, a Najeriya.

NAJERIYA: Yadda Kashe-kashen Kabilanci Da Na Addini, Boko Haram Da ‘Yan Bindiga Su Ka Bindige Zaman Lafiya

Yayin da shekaru barkatai ana fama da kashe-kashen kabilanci da rikice-rikicen addini, bullowar Boko Haram ya maida sauran kashe-kashen kamar wasan kwaikwayo.

Cikin shekaru 10 Allah kadai ya sa yawan dubban mutanen da yakin Boko Haram ya ci rayukan su. An kashe sojoji masu tarin yawa. An fasa garuruwa, an tarwatsa kauyuka. Sama da mutum milyan daya sun fada zaman gudun hijira. Sannan dubban kananan yara sun zama marayu.

Rikice-rikicen ‘yan bindiga, mahara da masu gsrkuwa da mutane sun kara dagula al’amurra. Matsalolin sun yi dagulewar da su na neman su fi karfin gwamnati.

Tunanin cewa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari za ta magance matsalolin da ta yi alkawari, an koma ana ganin cewa abin ya zama mafarki ko ma tatsuniya. Domin lamura sai kara rincabewa su ke yi.

Da yawa na ganin cewa jam’iyyar APC ta yaudari al’ummar Najeriya a zaben 2015, lokacin da ta buga tambarin kawo canji. Mafi yawa sun gaskata ta. Bayan an zabi jam’iyyar ta kafa gwamnati, ana ganin wadda aka rika yaba wa sallah, sai ta shi ta shiga limanci ashe ko alwala ba ta iya ba.

Yayin da Najeriya ta cika shekaru 60 da samun ‘yanci, hankulan jama’a sun fi damuwa ne wajen neman mafitar masifu, bala’o’i, matsaloli da dimbin kalubalen da su ka dabaibaye kasar.

Ko za a iya warware su nan kusa, ko kuma sai nan da wasu shekaru 60, wannan kuma shi ne abin da kowa ke kwana ya na tashi da shi a zukata.

Share.

game da Author