SHEKARU 60 BAYAN ‘YANCI: Buhari ya yi tilawar salsalar matsalolin Najeriya, ya auna farashin fetur a sikelin Nijar, Ghana da Chadi

0

Shugaba Muhammdu Buhari ya yi tilawar musabbabin shigar Najeriya matsalolin da ta tsince kan ta a ciki, ko aka jefa ta, tare da yin kiran cewa sai an taru an haɗa kai za a iya tsira tare.

A jawabin sa na cikar Najeriya shekaru 60, Buhari wanda ya yi jawabi daga Fadar Shugaban Kasa, ya ce, “tilas sai mun waiwayi baya, yadda mu ka tsinci kan mu a inda mu ke a yanzu, kafin mu iya dafa tudun-mun-tsira.”

Buhari, wanda a farkon jawabin sa ya kara jaddada godiyar sa ga ƴan Najeriya, bisa gasgata shi da su ka yi har su ka damka masa amanar mulki zango biyu, ya fara waiwaye yadda Najeriya ta ke a lokacin da a ka samu ƴanci, a 1960.

“Lokacin da aka samu ƴanci a 1960, adadin ƴan Najeriya ba su wuce mutum milyan 45 ba. A cikin mu din ma, milyan 7 ne kadai ke zaune a birane. Saura duk a karkara da kananan garuruwa su ke.

“Amma a yau yawan mu ya kai sama da mutum milyan 200. Kuma kashi 52% na yawan wadannan mutane (wato mutum milyan 104) duk a birane ko garuruwa su ke zaune.

“Idan mu ka dubi yadda iyayen kasar masu kishi su ka gina kasa bayan sun kwato mata ‘yanci, to sai mu dubi kan mu. Shin mun yi gaskiya da kishi da rikon amana, kamar yadda na bayan mu ɗin su ka yi?” Inji Buhari.

Daga nan ya fara kawo wadansu cikas ɗin da Najeriya ta fara cin karo da su bayan samun ƴanci.

Buhari ya bayyana cikas irin su Yaƙin Basasa da aka yi watanni 30 ana fafatawa. Sai kuma shekaru 29 da Najeriya ta shafe a karkashin mulkin soja.

“Haka nan da tafiya ta yi tafiya, tsarin ma’aikatan gwamnati, ƴan sanda, alkalai da sojoji sun sun tabarbare.

“Don haka tilas sai mun fara warkar da mikin da ke jikin kasar nan domin su tsira daga halin da ake ciki.

“Najeriya fa ba Shugaban Kasa ne ke da ita, ko shi ko ƴan adawa ba. Ta kowa ce. Saboda haka kowa ya tashi tsaye, aiki ne na mu baki daya.” Inji Buhari.

Daga nan sai ya koma ya fara jero wasu ayyukan ciyar da al’umma gaba da ya ce gwamnatin sa ta samar, ciki har da su TraderMoni, Shirin Samar da Aiki Ga Mutum Milyan 100 nan da shekaru 10 da sauran su.

Batun Farashin Litar Fetur:

A kokarin Buhari na kare karin kudin fetur da aka yi zuwa lita daya a naira 161, Buhari ya auna cewa, ana sayen lita daya kan Naira 362 a Chadi, Naira 346 a Jamhuriyar Nijar, Naira 326 a Ghana, Naira 211 a Egypt da kuma Naira 168 a Saudiyya.

Dukkan wadannan kasashe inji Buhari, duk su na haƙo man fetur su ma, inji Buhari.

Share.

game da Author