A ranar Talata din nan ce Saudiyya ta shiga cikin kasashen da ke yin tir da goyon bayan da Shugaban Faransa ya nuna cewa mujallar Charlie Hebdo na da ƴancin yin zanen ɓatanci ga Annabi (SAW).
Ma’aikatar Hulɗodin Kasashen Wajen Saudiyya ta yi tir da ƙoƙarin danganta addinin musulunci da ta’addanci. Kuma ta yi Allah-wadai da zanen ɓatanci da mujallar Charlie Hebdo ta yi ga Annabi (SAW).
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya goyi bayan zanen cewa masu yi na da ƴancin yin hakan.
Kasashen musulmi da dama da cibiyoyin Musulunci, ciki har da Jami’ar Azhar mai bin tafarkin Sunni, duk sun yi wa Faransa tofin Allah-wadai.
Tuni ana ta kiraye-kirayen kaurace wa kayayyakin kasar Faransa a duniya.
Wannan kamfen ya na ci gaba da tasiri sosai a duniyar Musulunci a soshiyal midiya.
Ba wannan ne karo na farko ba da Chalie Hebdo ya yi zanen ɓatanci kan Annabi (SAW).
Cikin 2015 da kuma shekaru da dama a baya duk mujallar ta yi.
Kasar Saudi dai a yanzu ta ce ba za ta daina yir tir da waɗanda su ka yi, ko su ka goyi bayan yin ɓatanci ga Annabi SAW ba, ko ma ɓatanci ga kowane Annabi.
Goyon bayan da Macron ya nuna cewa ƴanci ɗan Adam ne lamarin, ya biyo bayan kisan da aka yi wa wani malami ɗan kasar Faransa, wanda ya goyi bayan yin zanen ɓatanci.
An tsinci gawar malamin bayan an fille kan sa, abin da ya harzuka shugaban Faransa, har gwamnatin kasar ta karrama gawar malamin kafin a rufe ta.