SATAR ABINCI: Gwamnatin Kaduna ta bada odar kamo wadanda su ka yi wa rumbun ajiya kayan tallafi karkaf

0

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce za ta binciko kuma ta kamo, sannan ta hukunta wadanda su ka fasa rumbun ajiyar kayan tallafi a ranar Asabar.

Mataimakiyar Gwamna, Hadiza Balarabe, wadda kuma ke rikon akalar gwamna a yanzu, ita ce ta bayyana haka a jawabin da ta yi wa al’ummar jihar a ranar Lahadi.

Ta ce jami’an tsaro har sun fara kamo wasu da su ka kwashi kayayyakin.

“Babu wata kwana-kwana, duk wanda ya kwashi kayan tallafi na CACOVID, sunan sa barawo. Babu wani dalili ko uzirin da mutum zai bayar wai ya bada hujjar kwasar kayan.

“Jihar Kaduna ta sha alwashin bankado wadanda su ka saci kayayyakin ta hukunta su.” Inji Hadiza.

Ta ce hatta masu tunzira jama’a su kwashi kayan mutane, su ma su saurari fushin hukuma.

Ta ce an kakaba dokar-ta-baci a Kaduna domin wanzar da zaman kafiya a jihar.

Sannan ta gode wa sarakunan gargajiya da kuma jama’ar da su ka nuna da’a, wadanda ba su biye wa batagari an kwashi kaya tare da su ba.

A wani labarin a Kaduna, Hukumar Yaki da Shan Muggan Kwayoyi ta Jihar Kaduna, ta yi gargadin cewa kada jama’a su kuskura su yi amfani da kwayoyin magungunan da masu ‘wasoson ganimar kayan gwamnati’ su ka kwashe daga rumbun ajiyar Hukumar NAFDAC a Kaduna.

Babban Daraktan hukumar Joseph Maigari ne ya bayyana haka, cikin wata sanarwar da ya fitar ga manema labarai a ranar Litinin a Kaduna.

An ruwaito cewa an kwashe muggan kwayoyin da NAFDAC ta kama tare da magungunan da wa’adin aiki da su ya wuce tuni, Amma duk aka kwashe su karkaf a ranar Asabar.

Maigari ya ce masu kwasar kayayyakin sun yi awon-gaba da katan-katan na kwayoyin Tramadol da kwalayen kwalaben kodin.

Maigari ya ce duk wanda ya kuskura ya yi amfani da magungunan ba bisa ka’ida ba, to karshen sa kwarkwancewa, zautuwa da kuma birkicewar kwakwalwa.

“Duk wanda ya dade ya na sha, ko ya sha da yawa, zai zautu, ya rika zabura, ya na jijjiga da karkarwa da fizge-fizgen da ka karasa shi haukacewa tuburan.

“Haka mai fama da wata damuwa idan ya yi amfani da magungunan, to karshen sa karasa afkawa tunanin kokarin kawo nesa kusa, dawurwurar tunani da kuma hargitsewar tunanin da babu makawa sai haukacewa kawai.

“Kai, magungunan za su iya lalata hantar mutum, su kawo masa cikar wajen yin nunfarfashi, yadda numfasawa zai gagare shi, har ya rika shidewa, ya na suma. Daga nan kuma sai jijjige-jijjigen barin duniya, saboda babu makawa sai mutuwa kenan.” Inji Maigari.

Ya roki jami’an tsaro su gaggauta gano inda aka rika kai maganin.Sannan ya gargadi jama’a a yi kaffa-kaffa da sayen magani a hannun masu sayar da ‘danyen kaya.’

Maigari ya ce iyaye su kula da ‘ya’yan su sosai kada su rika amfani da muggan kwayoyi.

Share.

game da Author