Hukumar Yaki da Shan Muggan Kwayoyi ta Jihar Kaduna, ta yi gargadin cewa kada jama’a su kuskura su yi amfani da kwayoyin magungunan da masu ‘wasoson ganimar kayan gwamnati’ su ka kwashe daga rumbun ajiyar Hukumar NAFDAC a Kaduna.
Babban Daraktan hukumar Joseph Maigari ne ya bayyana haka, cikin wata sanarwar da ya fitar ga manema labarai a ranar Litinin a Kaduna.
An ruwaito cewa an kwashe muggan kwayoyin da NAFDAC ta kama tare da magungunan da wa’adin aiki da su ya wuce tuni, Amma duk aka kwashe su karkaf a ranar Asabar.
Maigari ya ce masu kwasar kayayyakin sun yi awon-gaba da katan-katan na kwayoyin Tramadol da kwalayen kwalaben kodin.
Maigari ya ce duk wanda ya kuskura ya yi amfani da magungunan ba bisa ka’ida ba, to karshen sa kwarkwancewa, zautuwa da kuma birkicewar kwakwalwa.
“Duk wanda ya dade ya na sha, ko ya sha da yawa, zai zautu, ya rika zabura, ya na jijjiga da karkarwa da fizge-fizgen da ka karasa shi haukacewa tuburan.
“Haka mai fama da wata damuwa idan ya yi amfani da magungunan, to karshen sa karasa afkawa tunanin kokarin kawo nesa kusa, dawurwurar tunani da kuma hargitsewar tunanin da babu makawa sai haukacewa kawai.
“Kai, magungunan za su iya lalata hantar mutum, su kawo masa cikar wajen yin nunfarfashi, yadda numfasawa zai gagare shi, har ya rika shidewa, ya na suma. Daga nan kuma sai jijjige-jijjigen barin duniya, saboda babu makawa sai mutuwa kenan.” Inji Maigari.
Ya roki jami’an tsaro su gaggauta gano inda aka rika kai maganin.Sannan ya gargadi jama’a a yi kaffa-kaffa da sayen magani a hannun masu sayar da ‘danyen kaya.’
Maigari ya ce iyaye su kula da ‘ya’yan su sosai kada su rika amfani da muggan kwayoyi.