Wasu masu zanga-zanga a Maiduguri, babban birnin Jihar Barno, sun fito kan titi su na nuna rashin amincewa da rushe ‘Yan Sandan Gaggawar Dakile Fashi da Makami ba, wato SARS.
SARS, wadanda a Turance ake kira da Special Anti-Robbery Squard, an rushe su a ranar Lahadi, bayan da zanga-zanga ta yi tsanani a wasu manyan garuruwan kasar nan, ana kiraye-kirayen rushe su.
Masu zanga-zanga sun nuna gajiyawa da irin yadda jami’an SARS ke wuce gona da iri, wajen azabtar da mutane da kisa ba bisa tsarin da dokar kasa ta gindaya ba.
Sai dai kuma a jihar Barno, wasu fitowa kan titi su ka yi, domin nuna rashin goyon bayan rusa SARS da aka yi.
‘Amfanin SARS A Barno’ – Ahmed Shehu
Zanga-zangar Barno ta kunshi gamayyar kungiyoyi da su ka hada da Kungiyar Lauyoyi, Reshen Jihar Barno, Kungiyoyin ‘Yan Kasuwa, Kungiyoyin Dalibai.
Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Kare Jama’a na Jihar Barno, Ahmed Shehu, ya ce su a Jihar Barno su na ganin amfanin SARS fiye da sauran jihohi.
“Idan ba a ganin amfanin su a kudancin kasar nan, to mu nan a Arewa mu na ganin amfanin su.
“Kowa ya san yadda matsalar tsaro ta ke a fadin jihar Barno. Yanzu haka daga Maiduguri kowa na tsoron fita zuwa ‘yan garuruwan wajen birni ko kauyukan da ke kusanci da Maiduguri.
“Kowa ya san irin kokarin da Gwamnatin Jiha da Gwamnatin Tarayya ke yi wajen samar da tsaro. Amma a gaskiya har yanzu babu tsaron nan.
“Idan kungiyoyin agaji za su je kowace Karamar Hukuma, sai da jami’an tsaro. Kuma banda SARS babu wasu jami’an da ke iya yi masu rakiya.
“Duk wani shingen jami’an tsaro a Barno, SARS ne ke kula da shi, ba game-garin ‘yan sanda ba.
“SARS ne fa su ka ceci mutane ranar da aka kai wa tawagar Gwamna Zulum hari. Shi ya sa mu ka cika da mamaki jin cewa an rushe SARS.
“Mu ma mun damu da korafe-korafen da jama’a a sauran sassa ke yi a kan SARS, amma dai mu a Arewa maso Gabas, har gara a kwaso jami’an SARS a jihohin da ba a son su a kawo mana su nan.
Saboda mun san idan babu su, kuma babu wasu madadin su, to ba da dadewa ba za su yaba wa aya zaki.” Inji Shehu.
Daga nan sun yi tattaki zuwa cikin Gidan Gwamnati, inda Mataimakin Gwamna Umar Kadafur ya karbi wasikar su.
Kadafur ya jinjina masu tare da alwashin za a mika kukan su inda ya dace.