SAKE FASALIN SARS: Kwamitin Shugaban Kasa ya bada sunayen fitinannun ƴan sanda 37 da za a kora, a hukunta wasu 24

0

Kwamitin Shugaban Kasa mai Sake Fasalin SARS ya bada sunayen wasu fitinannun jami’an SARS 37 da ya bada shawarar a kora daga aiki, saboda samun su da aka yi da laifin take hakkin jama’a. Akwai wasu 24 da su ma wasu gungun batagarin jami’an SARS din ne da kwamitin ya ce a gurdanar da su a kotu a hukunta su.

Hakan ya bayo bayan wani bincike da kwamitin ya gudanar, bayan ya karfi korafe korafe har 113 daga jama’a daban-daban.

Kakakin Yada Labaran Hukumar Kula da Aikin Dan Sanda ta Kasa (PSC) ce ya sanar da haka, cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Juma’a, a Lagos.

Shugaban Hukumar Kare Hakkin Jama’a, Tony Ojukwu ne ya nemi hadin kan hukumar ta PSC da ta tattaba tabbatar da korar baragurbin ‘yan SARS din, sai kuma gurfanar da wasu fitinan 24 a kotu.

Ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya ke gabatar da sakamakon rahoton kwamitin binciken da Buhari ya korafe korafen da aka rika yi kan SARS, tun cikin 2018.

“Mun zo domin mu mika bukatar mu ga Hukumar Kula da Aikin Dan Sanda, wadda ita ce ke da hakkin hukunta wadanda kwamiti su ka kama da laifi.” Inji Ojukwu.

Kwamitin ya kuma bukaci Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Muhammad Adamu ya fallasa sunayen wasu ‘yan sanda 22 da aka bada rahoton yadda su ka ci zarafin jama’a.

Shugaban Hukumar Kula da Aikin ‘Yan Sanda, Musuliu Smith, ya tabbatar wa Hukumar Kare Hakkin Dan Adam cewa su taimaka wajen sa hannu a gyara aikin dan sanda. Ya ce za a bayar da horo sosai da kuma tantance wadanda za a yi gyaran da su, don gudun kada a sake daukar batagari, irin wadanda su ka janyo wa SARS bakin jinin da aka rusa su baki daya.

Share.

game da Author