Saboda matasan Arewa sun yi wa malamai biyayya da da’a ga shugabanni shine ya sa Aisha Yesufu ta kira su wawaye? Daga Maryam Yamusa

0

Kalaman da ya fito daga bakin fitacciyar ‘yar gwagwarmaya Aisha Yesufu kan matasan Arewa ya bani, inda ta tsagalgale tana sur-surfa musu zagi saboda ba su bi sahun matasan kudu sun babbake jihohin su ya tada min da hankali matuka da yi mata addu’ar Allah ya shiryeta.

Idan Aisha bata sani duk tsagerancin dan Arewa da rashin kunyar sa, addinin sa da karantarwar Alkur’ani ne ke yi masa jagora.

Irin kalaman da Aisha ta yi akan matasan Arewa tana ciccin magani ta na zubda kalamai yadda take so. Ta kira sunan shugaba dattijo domin kawai yana shugabancin Najeriya wanda yayi jika da ita ta yi masa izgilanci sannan tana ganin hakan ne cigaba da kare ‘yancin mutane toh ta sani, ta yi a banza domin babu wanda ya dauke ta mai kangado a yankin Arewa.

Duk wanda zai fito ya rika zuga matasa su yi wa shugabannin sa bore, ya rika sabawa kiran malamai ba mutumin da za rika saurara bane ko kuma a rika bi.

A wani bidiyo da na gani Aisha ta yi ta saka a shafukan yanar gizo, ta rika ragargazar dattawan Arewa da Sarakunan mu, tana caccakar matasa da sauran mutanen Arewa saboda biyayya da dokokin Allah da shugabanni.

Ita dai da ta ga yin hakan shine yafi dacewa mata sai ta maida hankali, mu tarbiyyar mu bai koyar da mu haka ba. duk lalalcewar mutane suna ganin darajar nagaba a yankin Arewa. Ba fitsara da nuna jijiyoyin wuya bane gwagwarmaya, da kutsawa cikin maza ana ta haki da ife-ife ne jarumta.

Ni a nawa ganin matasan Arewa basu bukatar shawara daga wurin mutane irin ta, tunda tunda ake kashe mutane a yankunan Arewa bata taba zuwa yankin ta kira matasa su fito su yi zanga-zangar hana kisan ba. Wadanda suka fito ma ba a taba ganinta ta zo ta shiga cikin su ba tana gwagwarmaya, sai ta caske a Abuja tana ta ife-ife kawai na rashin kunya.

Ita dai da taga zata iya sai ta cigaba, zanga-zangar #EndSARS ne dai baza mu yi ba ta sani. Mu a Arewa mun yarda kuma mun amince cewa gwamnati ta amsa kiran su kuma tana kokarin biyan bukatunsu duka.

Share.

game da Author