Rushe SARS matakin farkon garambawul din da za mu yi wa Hukumar Ƴan Sanda ne -Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa rushe rundunar ƴan sandan SARS da aka yi a ranar Lahadi, shi ne matakin farko da gwamnatin tarayya ta ɗauka domin yin garambawul ga hukumar ƴan sanda.

Da ya ke jawabi wajen kaddama da Shirin Samar Wa Matasa Majiya Karfi Aiki su 774,000 (P-YES), Buhari ya ce bai tsaya ga rushe rundunar SARS kadai ba, ya kuma bada umarni a yi kwakkwaran bincike a gano wadanda su ka rika cin zarafin mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, a hukunta su.

“Zan yi amfani da wannan dama na yi bayani dangane da yadda ‘yan Najeriya su ka nuna hakikanin damuwar su dangane da yadda jami’an SARS ke kashe mutane ba bisa hakkin doka ba, da kuma yadda su ke cin zarafi da zaluntar wadanda ba su ji ba su gani ba.”

A wurin kaddamarwar har da Mataimakin Shugaba, Yemi Osinbajo, Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawal da Gwamna David Omahi.

“Rushe rundunar SARS da aka yi zai zama matakin farko na yi wa Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya garambawul din da zai kasance babban aikin su shi ne kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.

“Za mu tabbatar an yi bincike kuma an hukunta wadanda aka samu da laifi a cikin su.

“Ina bada hakuri da kuma jimamin rashin wadanda SARS su ka bindige.

“Amma kuma ya zama wajibi mu gane cewa akasarin ‘yan sanda mutanen kirki ne, masu kishi da aiki tukuru.

“Don haka ba za mu bari wasu tsirarun batagarin cikin su su janyo wa masu yawan cikin su bakin jini ba.” Inji Buhari.

Da ya koma kan Shirin P-YES, Buhari ya ce shirin na cikin tsare-tsaren da gwamnatin sa ta bijiro da su tun a 2016, na samar wa mutum milyan 100 aiki cikin shekaru 10.

Ya ce shirin zai rufa wa matasa 774,000 asiri, wadanda za a dauko daga Kananan Hukumomin kasar nan 774.

Buhari ya duba wasu kayan aikin da matasan za su yi aiki da su. Ya kuma jinjina wa Mashawarcin sa kan Matasa da ‘Yan Bautar Kasa, Nasiru Adahama, wanda ya ce shi ne kashin-bayan shirin.

Share.

game da Author