RASHIN TSARO: An yi garkuwa da Shugaban Karamar Hukuma da direban sa

0

Masu garkuwa da mutane sun yi wa Shugaban Karamar Hukumar Igammu ta cikin Jihar Oyo kwanton-bauna a jeji su ka yi gaba da shi.

An yi garkuwa da Jacob Adeleke da direban sa a ranar Lahadi da yamma, lokacin da su ke kan hanyar zuwa Ibadan.
An tabbatar cewa ya na kan hanyar zuwa Ibadan ne, domin taron shugabannin kananan hukumomin Oyo da Gwamna Seyi Makinde.

Kakakin ‘Yan Sandan Oyo, Olugbenga Fadeyi, ya tabbatar da garkuwar da aka yi da Shugaban Karamar Hukumar.

Ya ce an tare shi ne a kan hanyar Okon-Ado Awaye kafin ya kai Ibadan.

An sace shi rana daya da Hakimin Lingyado na cikin Karamar Hukumar Maru a Jihar Zamfara, wanda aka yi garkuwa da shi mako daya bayan mahara sun kashe mutum 22 a Karamar Hukumar Talata Mafara, Jihar Zamfara.

PREMIUM TIMES ta bada labarin an yi garkuwa da hakimi da wasu mutum biyu.

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Zamfara ta bada sanarwar cewa wasu gungun ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Hakimin Lingyado da ke cikin Karamar Hukumar Maru.

Kakakin ‘Yan Sanda na jihar, Mohammed Shehu ya ce ‘yan bindiga sun yi tattaki har gida su ka tafi da shi da karfin tsiya, a ranar Lahadi, wajen karfe 8 na safe.

Ya ce sun kuma yi gaba da wasu mutum hudu tare da Hakimin.

“Rundunar Hada-ka ta ‘yan sanda da sojoji da ke kusa da garin ta kai daukin gaggawa bayan da aka sanar da ita cewa ‘yan bindigar sun isa garin.

“Ba don gaggawar da jami’an tsaron su ka yi ba, da wadanda masu garkuwa za su tafi da su, su na da yawa sosai.”

Haka Mohammed Shehu ya sanar a sanarwar manema labarai da ya fitar, kuma bai bayyana sunan Hakimin da sauran mutum hudu da aka gudu da su ba.

Amma dai jama’ar gari sun tabbatar da sunan hakimin Dalha Danjago.

Kakakin ‘yan sanda ya yi kira ga jama’a su kai rahoton duk wani motsi da ba su amince da shi ba.

Ya ce ‘yan sanda da sojoji sun bazama cikin dazuka domin ceto hakimin da sauran mutum hudu da aka yi garkuwa da su tare.

Wannan al’amari ya zo mako daya bayan da ‘yan bindiga su ka kashe mutum 22 a kauye daya a rana daya, kuma a lokaci daya a Zamfara.

Dangane da kokarin gano Shugaban Karamar Hukuma a Oyo kuwa, ‘yan sandan jihar sun baza jami’an su cikin dazuka, domin ceto Adeleke da direban sa.

Share.

game da Author