RASHIN TSARO: Ƴan bindiga sun arce da matar kwamandan ‘yan bijilante da dan sa Jigawa

0

Ƴan bindiga sun shiga har cikin Dutse, babban birnin Jihar Jigawa, su ka yi awon gaba da matar Mataimakin Kwamandan Ƴan Bijilante, Abdullahi Suleiman da kuma dan sa.

Rundunar ‘yan sandan Jigawa ta tabbatar da haka, tare da cewa amma sun ceto dan, saura matar ce ta rage a hannun masu garkuwar.

Mazauna unguwar sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan bindigar sun je har gidan Mataimakin Kwamandan da ke Galamawa, kan titin zuwa filin jirgin saman Dutse, wajen 12 na dare.

Unguwar ta na kusa da Kachi, Limawa kan hanyar filin Jirgin Sama na Dutse, kuma ya na kusa da wani sansanin sojoji da ke Fanisau.

Lamarin ya tsorata mazauna garin, ganin wannan ne karo na farko da aka yi garkuwa da wani a garin.

Sunan wadda aka yi garkuwar da ita Husna, kuma dan na ta Umar, dan shekara tara ne, ita kuma Husna mai shekaru 50.

Mazauna wurin sun ce mai yiwuwa dama masu garkuwar na fakon mijin ta, wanda shi ne mataimakin kwamandan ‘yan bijilante a jihar Jigawa.

Lokacin da lamarin ya faru maigidan ba ya nan. Shi kuma Kakakin Yada Labarai na ‘yan sandan Jigawa, Abdul Jinjiri, ya ce ‘yan sanda sun bi masu garkwar a guje, su ka bar dan a tilas, amma su ka tsere da uwar.

Ya ce su na ta kokarin gano inda ta ke domin ceto ta. Sannan ya roki jama’a su kai rahoton duk wani da su ke ganin ba su amince da shi ba, ko kuma su ka ji kishin-kishin din inda aka yi garkuwa.

An yi garkuwa da matar a rana daya da yin garkuwa da Hakimin Lingyado na Karamar Hukumar Maru da ke jihar Zamfara.

Kuwa a ranar ce aka yi garkuwa da wani Shugaban Karamar Hukumar a Jihar Oyo.

Share.

game da Author