Nan da shekaru biyu masu zuwa Najeriya za ta haramta sha da shigo da madarar kasashen waje. Haka dai Ministan Ma’aikatar Gona, Sabo Nanono ya bayyana.
Ministan ya yi wannan jawabin a taron Tunawa da Ranar Abinci ta Duniya, a Abuja.
“Ku rubuta ku ajiye, nan da shekaru biyu za mu daina shigo da madara daga kasashen waje.
“Mu na da akalla shanu milyan 25 a kasar nan, sannan shanun nan da yawan masana’antun sarrafa madara sun kai akalla darajar naira tiriliyan 33. A kullum ana shan madara lita milyan biyar a Najeriya.”
Nanono ya ce nan ba da dadewa ba Najeriya za ta yi adabo da yunwa da talauci ta hanyar bunkasa yalwar abinci da kiwo.
Ya ce a yanzu Najeriya ce ta daya wajen noma shinkafa mai tarin yawa, ba don komai ba, saboda an hana shigo da shinkafa daga waje, ana noma dukkan wadda ake amfani da ita a nan Najeriya.
Wannan gwamnati ta bada himma wajen bunkasa noma, ta yadda kakaf yanzu a Afrika babu kamar Najeriya wajen noman shinkafa. Haka nan kuma Najeriya ce kasar da ta fi noma rogo a duniya, duk albarkacin himma da hobbasan da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi.”
Ya ce a yanzu haka Ma’aikatar Harkokin Noma ta tanadi kayan abinci mai tarin yawan metrik tan 109,567, kuma ana kyautata yakinin nan da karshen 2020 yawan abincin da ke ajiye a rumbunan Ma’aikatar Harkokin Noma zai rubanya zuwa tan 219,900.” Cewar Nanono.
Nanono ya yi dogon bayanin yadda wannan gwamnati ta samar da aikin yi ta fannonin noma daban-daban da kuma bunkasa abinci da fatattakar yunwa da kuncin fatara da talauci duk a lokaci guda.
Discussion about this post