Obasanjo, Ooni na Ife sun tofa baki kan zanga-zangar #EndSARS

0

Basarake Ooni na Ife, Adeyeye Ogunwusi, ya karɓi baƙuncin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, tare da rokon masu zanga-zangar #EndSARS su tsaida zanga-zanga haka nan.

Basaraken ya yi wannan rokon a fadar sa ta Oodua Palace, a garin Ike-Ife, inda ya bayyana zanga-zangar #EndSARS a matsayin wani sako na musamman daga matasan kasar nan zuwa ga gwamnati.

Ya roki matasa su hakura haka nan, su bai wa gwamnati lokaci somin ta samu damar gaggauta cika dukkan sharuddan da masu zanga-zanga din su ka gindaya mata.

“Idan ku ka kalli yadda zanga-zangar #EndSARS ke tafiya, za ku fahimci cewa matasan nan da kwazon iya mulkin kasar nan.

“A kullum dare su kan bayyana adadin yawan kudaden da su ka kashe da kuma adadin kudaden da su ka samu da adadin kudaden da su ka rage masu. Wannan ya nuna su na da kyakkyawar dabi’ar shugabanci da kuma yin taka-tsantsan da kudade.

“Haba matasa, ku yi hakuri mana, ku daina zanga-zangar nan haka nan, don gudun kada masu wata boyayyar manufa su kwace ragamar zanga-zangar lumanar da ku ke yi.”

Da ya ke magana kan harin da aka kai wa Gwamna Gboyega Oyetola na Osun, a wurin taron zanga-zangar #EndSARS, basaraken cewa ya yi abin takaici ne kwarai.

Kafin nan sai da Obasanjo ya nuna cewa zanga-zangar #EndSARS wani motsi ne mai nuna matasan kasar nan da ke zanga-zanga su na bukatar gwamnati ta saurare su day kunnuwan basira.

“Sama da Kashi 65 bisa 100 na yawan al’ummar kasar nan duk matasa ne daga shekaru 18 zuwa 30. Ba ilmi kadai su ke ta gaganiyar nema ba. Su na kuma hakilon nema wa kan su rayuwa mai inganci.

“To yawancin wadannan matasa ba su samu damar yin ilmi ba. Wadanda su ka gi kararun kuma ba su samu damar cin moriyar karatun da su ka yi ba.

“Ina da yakinin cewa idan gwamnati ta tsaya ta saurare su, ta nuna kulawa da su, hakan zai fi zama alheri.” Inji Obasanjo.

Share.

game da Author