Obasanjo, IBB, Gowon, Shonekan, Jonathan sun yabawa Buhari kan matakan da ya dauka don kawo karshen zanga-zangar #EndSARS

0

Bayan ganawar musamman da shugaban Ksa Muhammadu Buhari yayi da tsoffin shugabannin kasar nan kan matsayar da gwamnati ta dauka game da kawo karshen zanga-zangar #EndSARS, gaba dayansu sun amince da matakan da gwamnati ta dauka.

Idan ba a manta ba shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana a jawabi da yayi wa ‘yan Najeriya ranar Alhamis cewa gwamnati na bi dadki-daki domin biyan bukatun da masu zanga-zangar #EndSARS.

Buhari ya ce gwamnati ba za ta sa ido ta bari a sanadiyyar wannan zanga-zanga na #EndSARS kasa najeriya ta gagara zama ba.

Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa bayan sauraren Buhari da suka yi sun amince ta duka matakan da gwamnatin sa ta dauka domin kawo karshen ta’addanci da wasu matasa suke yi a wasu jihohin kasar nan.

Buhari ya ce bukatun su biyar da suka nemi a biya musu, duk gwamnati ta fara biyan su daya bayan daya kuma hatta tsuffin shugabannin kasar shaidu ne.

A karshe shugabannin sun yi kira ga matasan Najeriya su hakura hakanan su koma gidajen su su bari gwamnati ta iya ci gaba da kokarin kawo gyara da sauye-sauye masu ma’ana a kasar nan.

Share.

game da Author