Ranar Talatar da ta gabata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya rubuta wa Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila wasikar neman Majalisa ta amince ya bai wa wasu jihohi 5 kudaden da su ke bin gwamnatin tarayya bashi, har naira bilyan 148.
Jihohin da suka hada da Ondo, jihar da za a yi zabe nan da kwanaki bakwai kacal, za a ba ta naira bilyan 7.
Sauran jihohin sun hada da Bayelsa, Cross River, Osun da kuma Ribas.
Ga dalla-dallar yadda Buhari ya rika bai wa jihohin APC kudade a jajibirin zaben gwamna:
1. JIHAR OSUN A ZABEN 2018:
Buhari ya rubuta wa Majalisa takarda ta amince kuma ya biya Jihar Osun naira bilyan 16.7, makonni biyu kafin zaben gwamna a jihar.
Ya ce kudaden da aka rika zabtare wa Osun ne tun a cikin 1995 da kuma cikin 2012.
Gwamna Gboyega Oyetola ne ya nemi a biya kudin domin ya biya albashin watanni uku da ake bin sa bashi.
Masu nazarin siyasa da ‘yan adawa sun yi tir, amma sai da Buhari ya bayar.
2. JIHAR KOGI A ZABEN 2019:
Kwanaki 3 rak kafin zaben gwamnan Kogi cikin 2019, Buhari ya biya Jihar Kogi cakin kudin alkawari (promissory note) har na naira bilyan 10.069. Ya ce kudaden bashi ne na ayyukan titinan gwamnatin tarayya da jihar ta yi a madadin tarayya, su ne aka biya jihar.
3. JIHAR ONDO A ZABEN 2016 da ya ke ‘yan adawa ke rike da mulki a lokacin, ba a biya ta bashi lokacin zabe, kamar yadda ake yi wa jihohin APC ba.
4. JIHAR EKITI A ZABEN 2018:
Jihar ta na hannun ‘yan adawa, Ayo Fayose, shi ma ba s biya jihar bashi jajibirin zabe, kamar yadda ake yi wa Gwamnonin APC ba.
5. JIHAR EDO A ZABEN 2020:
Ana saura kwanaki 4 zabe gwamnatin tarayya ta je ta raba wa mata 2,000 tallafin bunkasa kananan sana’o’i.
6. BAYELSA DA ANAMBRA ba a ba su kudade a zaben 2019 da 2017 na Anambra ba, saboda su na karkashin gwamnonin adawa.
7. ONDO A ZABEN GWAMNA 2020:
Buhari ya rubuta wasikar neman a bai wa Gwamna Rotimi Akeredolu na APC naira bilyan 7.
Tuni masu sharhin siyasa ke cewa wannan bai dace da akidun da Buhari ke tutiya da su ba, domin tamkar ya na raba kudaden ne domin a sayi kuri’u da sauran salon magudin zabe.
Discussion about this post