Najeriya za ta bukaci Dala biliyan 2.4 don kula da kare mutane daga Kanjamau – NACA

0

Hukumar dakile yaduwar cutar kanjamau NACA ta bayyana cewa Najeriya za ta bukaci Naira biliyan 2.4 don kula da wadanda ke dauke da kanjamau da kare mutane a cikin tsawon shekaru uku masu zuwa.

Shugaban hukumar Gambo Aliyu ya Sanar da haka a taron gabatar da bayanai game da matsayin cutar a kasar nan da aka yi a Abuja ranar Talata.

Aliyu ya ce Najeriya za ta yi amfani da wadannan kudade wajen kula da mutum miliyan 1.9 din dake fama da cutar sannan da karin wasu mutum 540,000 da za su kamu nan gaba.

Ya ce yin haka zai taimaka wajen cin ma burin UNAIDS na kawar da cutar a Najeriya nan da shekaran 2030.

Sakamakon kididdigar yawan mutanen dake dauke da cutar da aka gabatar a watan Maris 2019 ya nuna irin dinbin nasarorin da aka samu a wajen yaki da cutar.

An gudanar da bincike a shekaran 2018 kuma an kashe dala miliyan 100 wajen gudanar da wannan binciken.

An yi amfanin da ma’aikata 185 wajen yin wannan aiki na bincike sannan an gano cewa daga ciki an gano mutum miliyan 1.9 masu shekaru ƙasa da 64 dake dauke da cutar.

Sakmakon binciken ya nuna cewa an samu ragowar mutum kashi 40 bisa 100 na yawan mutanen da ke kamuwa da cutar.

Yawan dogaro da tallafin kasashen waje

Aliyu ya ce Najeriya ta kashe dala biliyan 6.2 wajen kula da kashi 60 bisa 100 na mutanen dake fama da kanjamau a kasar nan daga shekaran 2005 zuwa 2018.

Kashi 70 bisa yawan kudadden da aka yi amfani da su an same su ne daga kungiyoyin bada tallafi dake Kasashen waje.

Bayan haka hukumar NACA ta ce tana bukatan Naira miliyan 75 duk shekara domin kula da mutum miliyan 1.5 dake dauke da cutar a kasar nan.

Sannan gashi kudadden tallafi daga kasashen waje da kasan ke samu sun fara janyewa.

A dalilin haka Aliyu ya yi kira ga sauran sassan gwamnati da su hada hannu da gwamnatin tarayyar wajen samar da kudaden da za a bukata wajen yaki da yaduwar cutar Kanjamau.

Share.

game da Author