NAJERIYA: Kau da radadin talauci da samar wa matasa aiki yi ne kawai mafita – Tambuwal

0

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya bada shawarar cewa muddun ana so a samu cigaba da natsuwa a kasar nan, dole sai an kawo karshen radadin talauci ga mutanen gari a rashin aikin yi ga matasa.

Tambuwal ta magana ne a wajen taron kaddamar da wata gidauniya mai suna ‘Project 20 Million’ wanda mai taimaka masa kan kanana da matsakaitan masana’antu, Akibu Dalhatu ya wakilta.

” Ya kamata a ce aduk lokacin da za a shirya kasafin kudi ana gudanar da tarurrukan musayan ra’ayoyi tsakanin mahukunta da mutanen gari.

” Hakan zai ba mutane daman bin ayyukan da aka saka a kasafin kudin za ayi musu, sau da kafa,sannan suni diddigi.

” Idan aka yi haka zai sa mutane su zama suna da masaniya game da ayyukan da gwamnati ke yi a ko ina a fadin kasar nan.

” Idan aka duba za a ga cewa yanzu fa Najeriya a cukuikuye take cikin matsaloli da dama kamar su, kashe-kashen rayuka na babu gaira babu dalili, sannan kuma ga ayuukan ta’addanci, dabanci, sace-sace da cin zarafin mata.

” Ba za mu yi wa kan mu adalci ba idan ba mun fito muna fadin halin da kasa ke ciki bane domin samun mafita, in ba haka ba kuwa, gaba ba za ta yafe mana kan abubuwan da muka aikata a yanzu.

Ya kara da cewa tashin hankali da aka samu a dalilin zanga-zangar #EndSARS, tuni ne a gare mu cewa mu shiga taitayin mu tunda wuri kafin wankin hula ya kai shugabannin mu dare.

Share.

game da Author