Babalaje na Garin Remo, jihar Ogun, Joseph Ogunfuwa ya yi da-na-sanin yi wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari Kamfen ya zama shugaban kasa a 2015.
Ogunfuwa ya bayyana rashin jin dadin sa ga salon mulkin shugaba Buhari a wajen taron murnar zagoyowar ranar haihuwarsa a jihar Ogun.
” Buharin da na sani a baya , ba shi bane yanzu na gani. Dalilin sanin irin sa a baya ya sa na yi masa Kamfen har ya zama shugaban kasa a 2015, amma yanzu ba wannan Buharin bane. Ya baiwa ‘yan Najeriya kunya matuka, ba haka aka dauka ba.
” Abin yana yi min ciwo yanzu, jajircewa da na yi, da karfina, dukiya ta, da duk wani Iko da Allah ya bani, domin a lokacin na yi mishi ganin shine kadai zai iya ceto Najeriya daga halin da ta shiga cikin duka ‘yan takara, ashe ba girin-girin ba, tayi mai ne.
” A lokacin duk abokaina sun guje ni wasu ma sun dauka na zauce ne, saboda tsananin soyayya da nake yi maka da mara maka baya. Yanzu ni ne nake binsu in rokon su su yi hakuri irin abubuwan da na yi musu saboda kai a baya. Ashe sun fi ni gaskiya.
” A karshe dai ina baka shawara cewa har yanzu kana da sauran shekaru biyu da zaka tabuka wani abun da za mu iya kuri da shi muce ai gashi kayi wa mutane musamman talakawa.
ogunfuwa ya ce duk da shi cikakken kirista ne, yana nan daram tare da kungiyoyin asire-asire da yake ci da suka hada da Reformed Ogboni Fraternity Incorporated, The United Brothers of Friendship and Sisters of the Mysterious Ten, da Freemasonry.