Shugabar Hukumar NAFDAC, Mojisola Adeyeye, ta fallasa yadda ta gaji tulin bashi na naira bilyan 2.3 a hukumar.
Ta ce ta karbi ragamar shugabancin NAFDAC a lokacin da motocin hukumar kalilan ne ke aiki.
Ta bayyana haka a lokacin da ta ke bayani wurin kare kasafin NAFDAC na 2021, a gaban Kwamitin Harkokin Lafiya na Majalisar Tarayya, ranar Talata a Abuja.
Adeyeye ta ce ta karbi shugabancin NAFDAC cike da muradin inganta hukumar ta yadda za ta iya rike kan ta.
Amma dimbin basussukan da ta taras ana bin hukumar da kuma yadda kayan aiki su ka yi karanci, sun kashe mata guyawu.
Ta ce ya zuwa watan Yuni, NAFDAC ta tara naira bilyan 4, daga kudaden da ta ke sayar da fam, haraji, tara da kudaden da masana’antu ke biya, a matsayin haraji, har zuwa watan Yuni.
Sai dai kuma Shugaban Kwamitin Lafiya na Majalisar Tarayya, Yusuf Sunnunu ya umarci shugabar ta NAFDAC ta koma ta sake tsara yadda ta gabatar da kasafin NAFDAC din bisa tsari, domin ya yi saukin gabatarwa a wurin su.
An ce ta koma ranar 2 Ga Nusamba, tare da cikakken bayani a rubuce kan dalla-dallar kudaden da su ka shigo wa NAFDAC da kuma wadanda ta kashe.