Gwamnan jihar Barno Babagana Zulum ya gargadi masu kitsa tuggun shirya zanga-zanga a jihar cewa su kwana da shirin cewa gwamnatin sa ba za ta kyale su su cimma burin su ba.
Zulum yabshaida wa sarakunan jihar da wasu dattawan jihar cewa sun samu bayanan sirri cewa an shugi da wasu mutane cikin jihar domin su yi zanga-zangar kiyayya ga sojojin Najeriya da hare-haren Boko Haram.
Zulum ya ce tuni har an kama wadanda ake zargi da shirya wannan zanga-zanga.
” Mu a job har Barno ba za mu manta illar da zanga-zanga yayi mana ba. Sanadiyyar zanga-zanga saka hular Kwano ne ya haifar mana da Boko Haram, saboda haka ba za mu bari irin haka ya aake faruwa a jihar ba. Duk mai son shirya irin haka a Barno zai dandana kudar sa.
Bayan haka ministan Ayyukan Gona Baba shehuri wanda shima ya halarci wannan taro, ya mika sakon shugaban Kasa Muhammadu Buhari ga gwamnan Barno da mutanen jihar.
Shehuri ya ce shugaba Buhari ya yaba wa gwamnati bisa rabon gayan agajin Korona da ta yi wa mutanen jihar.
Baya ga kayan abinci, gwamnatin Barno ta raba wa mata da marasa karfi kudade.
Gwamnatin Zulum ta ce zata cigaba da rabawa mutanen Barno tallafi akai akai domin sama musu saukin rayuwa.