Mu maida hankali wajen daƙile yunwa da talauci, ba mu ɓuge wajen ƙaƙalen-son-iyawa ba – Osinbajo

0

Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa ƙaƙalen-son-iyawa da mahukunta a gwamnati ke yi wajen bata lokaci kafin a magance wata matsala ko tsaiko wajen ci gaban kasa, shi ne ke kara jefa kasar nan cikin maysaloli.

Osinbajo ya ce sai an maida hankali wajen gaggauta shawo kan matsalolin da aka rigaya aka san su kuma aka san hanyoyin magance su, ba wai a tsaya ana tsilla-tsilla, kewaye-kewaye da kakalen-son-iyawa ba.

Ya yi wannan furucin ne a wurin rufe taron kwana biyu na hadin-guiwar bangaren Majalisa da Masu Zartaswa, wato Ministoci da Manyan Gwamnati.

An shirya taron domin gano kalubalen da ke kawo cikas wajen saurin zartaswa da aiwatarwa tsakanin bangarorin gwamnatin biyu.

“Ai kowane tsari ya san hanya mafi dacewar da za a bi a samu nasara kan wasu kalubale.

“Misali, kowa ya san yunwa da fatara da talauci sun yi wa al’ummar kasar nan katutu. Sannan sannan kuma milyoyin kananan yara ba su da sukunin iya zuwa makaranta.

“Cutar korona ta kara daddasa hauhawar wadannan tulin matsalolin. To wannan ne matsalolin da ke gaban mu.

“Ashe kenan ba mu kyauta wa kan mu da kasar mu ba idan ba mu hada kai da hada hannu mun magance wadannan matsalolin da ke wa rayukan marasa galihu barazana ba.” Inji Osinbajo.

“Don haka mu maida hankali kan abin da aka zabe mu mu yi, ba mu buge wajen bata lokaci da kakalen-son-iyawa ba.”

Osinbajo ya ci gaba da buga misalai kan irin rawar da ‘yan Majalisa da ministoci ke takawa a kasashe daban-daban, domin ciyar da kasashen na su gaba.

Share.

game da Author