Gwamnatin Tarayya za ta fara yekuwar matakan rage faruwar bala’o’i a wuraren zaman jama’a da ma’aikatun gwamnati.
Ministar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya, Sadiya Farouq, ita ce bayyana haka a ranar Laraba a bikin Ranar Rage Aukuwar Bala’i ta Duniya ta shekarar 2020 wanda a kan yi a duk fadin duniya a kowace ranar 13 ga Oktoba.
A cewar Sadiya, za a yi yekuwar ne don ƙara fakakar da kamfanoni da ma’aikatu da ma sauran jama’ar kasa game da yadda za su kasance cikin shirin ko-ta-kwana tare da ɗaukar matakai don rage aukuwar bala’in gobara a dogayen benaye da gidajen masu yawan mutane da gine-gine mallakar jama’a da na gwamnati, da kuma wuraren aiki don tabbatar da cewa sun fito da tsarin ceton jama’a daga gobara tare da yin atisaye jefi-jefi kan yadda za a fice daga inda gobara ta barke.
Ministar ta ce, “Don tabbatar da hakan, wannan Ma’aikatar tare da hadin gwiwar hukumomin da aka dora wa alhakin kula da faruwar bala’o’i, za ta shirya atisaye na farko kan aikin ceto daga gobara a Ginin Sakatariyar Tarayya. Za a yi atisayen a ranar Juma’a, 23 ga Oktoba, 2020.
“Za a yi hakan ne domin a cikin shekarar 2020 kadai, Nijeriya ta gamu da bala’in gobara sama da guda ashirin a gine-ginen gwamnati da na jama’a. Saboda haka gobara na daga cikin manyan bala’o’in da ake da su a Nijeriya.
“Manufar atisayen ceto daga gobara da za a yi a makon gobe ita ce a tabbatar da cewa an yi shirin amfani da hanyoyin ficewa daga Ginin Sakatariyar Tarayya idan gobara ta kama shi. Irin wannan atisayen zai bada damar ficewa cikin natsuwa tare da kauce wa rububi da hayaniya da akan yi a lokacin gobara, wanda hakan ya na jawo rasa rayuwa idan babban bala’in gobara ya faru.
“A yayin da hankulan mu su ka koma kan matsalar gobara a wannan rana, wannan Ma’aikata za ta ci gaba da fito da dabaru wadanda ba kawai faruwar daidaikun bala’o’i irin su gobara da ambaliyar ruwa za su yi aiki a kan su ba, har ma da wadanda kan faru a wasu kebantattun yanayi kamar bala’i a ma’aikatu irin su fashewar bututun mai da hujewar bututun iskar gas.”
Sadiya ta yi kira ga jama’a da su sanar da iyalan su da ofis-ofis din su darussan da za su koya daga atisayen da za a yi kan ceto daga gobara a mako mai zuwa, don ganin an magance aukuwar bala’i a Nijeriya.
Jigon bikin na bana dai shi ne, “Aikin Rage Aukuwar Bala’i”.
Tun daga lokacin da aka kirkiro ta a ranar 21 ga Agusta, 2019, wannan Ma’aikata ta yi ta fito da tsare-tsare da shirye-shirye wadanda za su taimaka wajen rage faruwar bala’i ko radadin sa a Nijeriya. Atisayen ceto daga gobara ma zai gaggauta tabbatar da tsarin rage bala’i a kasa.
Discussion about this post