Ministan Ilmi Adamu Adamu, ya bada umarnin gaggauta kafa kwamitin bincike wanda zai gano gaskiyar ko an daka wasoson naira bilyan 2.67 daga kudin ciyar da ‘yan makaranta a lokacin dokar zaman gida saboda Coronavirus a ma’aikatar sa.
Shugaban Hukumar ICPC ne, Bolaji Owasanoye ya yi ikirarin cewa an sace kudaden. “Maimakon a kashe kudaden wajen sayar wa yara masu karatu abinci, sai aka rika karkatar da kudaden aljifan wasu daidaikun mutane.
A kan haka ne Minista Adamu ya ce ya zama dole a gudanar da bincike domin a tabbatar da an karkatar da kudaden kuma a dakile yadda ba za a kara karkatar da wasu kudaden ba.
HARKALLAR NAIRA BILYAN 2.67: Jami’an Ma’aikatar Ilmi Sun Fara Walle-walle
Jim kadan bayan da Ministan Ilmi Adamu ya bada umarnin a yi binciken yadda aka ce an karkatar da kudaden, sai jami’an Ma’aikatar Ilmi su ka fara fito da wani zance daban.
Manyan jami’an harkokin ilmi sun ce tabbas an biya kudaden aljihun wasu mutane a lokacin zaman gida tilas saboda korona, amma ba karkatar da su aka yi ba.
Sun ce e an yi biyan kudaden da masu aikin dafa abinci da masu bada kayan abincin ke bin gwamnati bashi tun kafin a fara zaman korona ba a biya su ba.
Jami’an sun ce to kudaden da su ke bi bashi ne aka biya su. Amma ba kudaden ciyarwar ne aka rika watanda da su ba.
Sun ce an biya kudaden ne ta aljifan wasu shugabannin makarantu, saboda Coronavirus yawancin wadanda su ka bayar da bashin kayan abincin, manoma ne da kananan ‘yan kasuwa da masu dafa abincin da ba su da takardun shaidar biyan haraji da sauran ka’idojin da banki ke bukata kafin ya tura kudaden a asusun ajiyar su.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin da Ministar Agaji da Jinkai, Sadiya Farouq ta nesanta kan ta da ma”aikatar da daga zargin sun karkatar da naira bilyan 2.57.