Minista Sadiya na so a yi dokar da za ta kula da lafiyar gajiyayyu

0

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji, da Inganta Rayuwa, Sadiya Farouq, ta yi kira da a kare hakkokin dattawan kasar nan.

Ministar ta yi kiran ne a lokacin da ake gudanar da taron Ranar Tsofaffi ta Duniya, wanda aka yi a Abuja a ranar 30 ga Satumba, 2020.

A taron, inda Sakataren Dindindin na ma’aikatar, Nura Alkali, ya wakilce ta, ministar ta ce mutane masu yawan shekaru su na taka muhimmiyar rawa a cikin al’umma a matsayin shugabanni, wadanda ke kular mana da al’adun mu, kuma abin koyi wadanda ya kamata a riƙa girmama su tare da yin haƙuri da su da ba su girma.

Ta ce, “Ranar Tsofaffi ta Duniya ta bana ta zo a kan kari, ganin cewar ana fama da cutar korona wadda ta shafi mutane masu yawan shekaru ƙwarai da gaske a duk fadin duniya.

“Annoba kan fi shafar mutane masu yawan shekaru tare da saka su cikin babban hadari domin cuta ta fi kama su, ta jiki da ta tunani tare da ja masu barnar kudi wanda ya hada da a zambace su tare da mantawa da su. Abin bakin ciki shi ne da yawan su cuta kan yi saurin kama su, sannan an fi nuna masu bambanci da cutarwa saboda rashin lafiya da sauran lamurran damuwa da kan shafi tsufa.

“A wannan rana da aka ware domin tunawa da mutane masu yawan shekaru, tare da kula da gudunmawar su da al’umma, ina kira a gare mu baki daya da mu girmama su, mu darajta su, kuma mu yi hakuri da su.

“Tsufa ba cuta ba ne ko kasawa, amma albarka ne kuma lokaci ne a rayuwa da duk mu ke so mu cimmawa.”

Sadiya ta gode wa mutane masu yawan shekaru saboda gudunmawar su wajen gina kasa, kuma ta tabbatar masu da cewa ma’aikatar ta za ta goya masu baya domin su samu saukin gudanar da rayuwar su.

Haka kuma ta nanata sadaukarwar gwamnati ga kafa tare da fara aiwatar da Cibiyar Tsofaffi ta Kasa (National Senior Citizen’s Centre) wadda ake sa ran za ta samar da horo da damarmaki wajen fito da ayyuka da shirye-shirye domin ‘yan kasa masu yawan shekaru.”

Jigon ranar ta bana shi ne “Annobobi: Su Na Sauya Yadda Mu Ke Kula Da Yawan Shekaru Da Tsufa Kuwa?”

Share.

game da Author