Kakakin fadar gwamnatin Zamfara, Bappa Zailani ya bayyana cewa cewa gwamnati Bello Matawalle ta kafa kwamiti domin bincikar wasu kudaden talakawan jihar Zamfara har naira bilyan 107 da gwamnati da ta gabata ta yi awon gaba da su.
Mataimakin gwamnan jihar, Mahdi Aliyu Gusau ne ya karanta matsayar gwamnati bayan ganawar majalisar zartaswar jihar.
Mahdi ya ce, wannan shawara ce da kwamitin da aka kafa tun farkon wannan mulki domin n ya binciki yadda Abdulaziz Yari ya kashe kuɗaɗen jihar.
Ya ce an gano wasu kuɗaɗe har nair biliyan 107 da suka bace bat, ba a san yadda aka yi da su ba.
” An gano cewa akwai wasu kuɗaɗe, naira bilyan 10 da gwamnatin Tarayya ta zuba a cikin asusun gwamnatin jihar, ta hanyar yanar gizo, cikin kwana biyu an neme su na rasa. Kwata-kwata ba a saka su cikin kuɗaɗen da suka shiga asusun jihar ba.
” Sannan an gano wasu kuɗaɗe naira bilyan 10 da aka saka cikin asusun wasu kamfanonin ƴan canji a Kano. Wadannan kuɗaɗe dai kamata yayi su shiga asusun gwamnatin jihar ne amma aka karkartar dasu.
Sannan kuma da wasu harkalla masu yawa na biliyoyin naira da duk bace babu su.
A karshe Matawalle ya ce yin wannan bincike ya zama dole saboda amanar da mutanen jihar Zamfara suka bashi. Ya ce ba zai saka ido ya bari a barnatar da kuɗaɗen talakawan jihar ba sannan bai yi komai a kai ba.
Kakakin Yari ya ce ba su tsoron wannan kwamiti saboda basu aikata duka abin da ake zarginsu da aikatawa ba.
” Ba gudu ba ja da baya, muna jiransu. ”