A cigaba da sace-sace da wasu fitsararrun matasa ke yi a fadin jihohin Kasar nan da wasu magidantan, a ranar Talata, wadannan matasa da mutane sun afka wa dakin ajiye kaya na hukumar kula da dalibai masu Bautar Kasa wato NYSC dake kubwa Abuja.
Wakilin PREMIUM TIMES ya ruwaito mana cewa barayin matasan sun dira ofishin NYSC ne tun da sanyi safe, da misalin karfe 8.
Sun rika jidar katifu, Babura da duk wani abin amfani da suka ci karo da da su a dakin ajiyar.
Sai dai ba da dadewa ba, jami’an tsaro suka kora su, inda suka nemi su yi arangama da su.Wakilin mu ya hangi wani dan iska da harsashi ya same shi a kafa abokan sa sun dauko shi ranga-ranga suna ife-ife.
PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda matasa da wasu magidanta suka farfasa dakunan ajiya har guda hudu a Abuja su yi awon gaba da kayan abinci da aka ajiye domin rabawa Talakawan Najeriya ranar Litini.
Barayin sun sace babura, Atamfofi, kayan abinci da sauran su.
A daidai matasan na aikata wannan ta’asa ne ministan Abuja ya umarci jami’an tsaro su kama wadanda suka fasa rumbun ajiyan abinci da kayan masarufi na tallafin Korona.
Jami’an Tsaro sun sanar da kama wasu daga cikin wadannan ‘yan iska.