Masu Zanga-zangar #EndSARS sun fatattaki Sowore a wurin Zanga-zanga

0

Masu Zanga-zangar #EndSARS sun fatattaki mawallafin jaridar SAHARA REPORTER a wurin zanga-zanga a Abuja.

Kamar yadda bidiyon abinda ya faru ya nuna, Sowore ya isa wurin zanga-zanga a motar sa. Sai dai bayan ya sauka zai kutsa cikin masu zanga-zanga sai suka fara yi masa Ihu, ” Ba mu so, ba mu so, yi tafiyar ka, yi tafiyarka

Haka dai masu kare shi suka tattare shi, suka saka shi cikin mota ya yi tafiyar sa.

Kwamitin Buhari ya amince a biya dukkan bukatu 5 na masu zanga-zangar rushe SARS

Taron da Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarni a gaggauta shiryawa a karkashin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, ya amince a biya dukkan bukatu biyar da masu zanga-zangar #EndSARS su ka gindaya wa Gwamnatin Tarayya.

Taron a karkashin Sufeto Janar Muhammad Adamu, ya samu halartar wakilan Hukumar Kare Hakkin Jama’a, Kungiyoyin Kare Hakkin Jama’a da kuma wakilan masu zanga-zanga.

Wasu daga cikin yarjejeniyar da aka amince da ita, sun hada da jami’an tsaro su daina jibgar masu zanga-zanga, kuma a saki dukkan wadanda aka kama.

Kakakin Yada Labarai na Shugaban Kasa, Femi Adesina ne ya turo wa PREMIUM TIMES dukkan abin da aka amince da shi a wurin taron kwamitin.

Jawabin Sufeto Janar Adamu ya jaddada matsayin gwamnati na kyale ‘yan Najeriya su rika yin zanga-zangar lumana, ba tare da gallazawar jami’an tsaro ba.

Sannan kuma ta na kan matsayin ta cewa rayukan ‘yan Najeriya na da matukar daraja. Kuma babban aikin dan sanda shi ne tsare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.

Sannan kuma za a gaggauta dawo da martaba, kima da darajar aikin dan sanda a kasar nan.

Kuma za a kafa gagarimin kwamiti wanda zai tsara kuma ya shata jadawalin yadda za a sake fasalin bai wa ‘yan sanda horo tun daga mataki na farko har zuwa ka’idojin yadda za su rika bincike da kama wanda ake zargi.

Wakilai da shugabannin kungiyoyin sa-kai na da kare hakki duk sun wakilta, har da Rafsanjani na CISLAC da Kole Shettima daga MAC Arthur.

Akwai kuma wakilin Ma’aikatar Kula da Harkokin ‘Yan Sanda ta Tarayya.

Share.

game da Author