Kwamishinan ‘Yan Sandan Abuja, Bala Ciroma, ya ce wadanda su ka kai wa masu zanga-zangar #EndSARS farmaki a Abuja, ba ‘yan iskan gari ba ne, masu goyon bayan SARS ne.
PREMIUM TIMES ta kawo rahonton yadda wasu da ake zargin zauna-gari-banza ne, su ka kai wa masu zanga-zangar #EndSARS farmaki, har su ka ragargaza motoci biyar.
Ciroma ya ce ba hari aka kai ba, taho-mu-gama ce, wato arangama tsakanin bangaren da ke goyon bayan SARS, su da wadanda son a ruguje su baki daya.
“Mun gano akwai zanga-zanga a Abuja. To daga nan kuma sai mu ka fahimci masu zanga-zanga sun kasu biyu.
Ya ce bangarorin biyu sun yi mummunar musayar zafafan kalamai, amma ba aka kashe kowa ba. Kuma jami’an tsaro sun shiga tsakani.
An shiga rana ta 7 ana zanga-zanga a Abuja. Masu zanga-zanga sun yi dandazo a Gadar Berger, su na kururuwar a sauya fasalin aikin ‘yan sanda.
Sun fara lafiya kalau amma wajen karfe 1 na rana sai wasu ‘yan daba dauke da sanduna da falankan katako su ka nemi tarwatsa su.
Sun rika lalata motocin da masu zanga-zanga su ajiye a gefen titi, kuma su na kai wa ‘yan #EndSARS hari.
Ana ci gaba da zanga-zanga duk kuwa da an rushe SARS, kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya sa a yi bincike, a gurfanar da jami’an da su ka wuce gona-da-iri, su ka rik yake hakkin jama’a.
Discussion about this post