Manyan makarantun jihar Kano za su koma karatu ranar 26 ga Oktoba

0

Gwamnatin jihar Kano ta sanar cewa duka manyan makarantu mallakan jihar za su dawo aiki daga ranar 26 ga Oktoba.

Kwamishinan ilimi Mariya Mahmoud ta Sanar da haka ranar Litini a garin Kano.

Ta ce gwamnati ta yanke shawarar bude manyan makarantun mallakar jihar ne bayan tattaunawa da ta yi da masu ruwa da tsaki a fannin ilimin jihar.

Mariya ta ce gwamnati ta yi wa makarantun feshin magani sannan ta raba kayan kare ma’aikatan kiwon lafiya daga kamuwa da cutar korona.

Yadda Ɗalibai zasu koma makarantu a Jihar Kano

Kwamishinan ilimin jihar Kano Muhammad Kiro ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta amince ɗalibai su koma makarantu domin ci gaba da karatu daga ranar 11 ga Oktoba.

Kwamishinan ya ce sai dai ba kamar yadda ake zuwa kullum ba a da ɗaliban za su yi.

Ya ce gwamnati ta tsara cewa ƴara ƴan makarantan firamaren aji 1 da na aji 2 za su rika zuwa makaranta ne a ranakun Litini da Talata kawai.

Sai kuma Ƴan aji 3, 4 da 5 za su rika zuwa a ranakun Laraba, Alhamis da Juma’a.

Su kuma wadanda za su shiga aji daya na karamar sakandare da aji daya na babban sakandare wato JSS 1 da SSS 1 za su yi jiran makonni 5 a gida har sai anngama zangon karatu da ya rage na sauran ajujuwan da suka saura.

Amma kuma ɗaliban ajujuwan JSS 2 da JSS 3 da kuma SSS 2 duk za su dawo karatu kamar sauran.

Haka suma makarantun Islamiya dake fadin jihar duk zasu koma karatu, amma kuma za su kiyaye sharuddan Korona da gwamnati ta saka.

Share.

game da Author