Mahara dauke da bindigogi sun kashe mutum shida a kauyen Kidandan, dake karamar hukumar Giwa, jihar Kaduna.
Maharan sun far wa kauyen ne ranar Juma’a da dadddare sannan suka sake dawowa ranar Asabar da rana tsaka.
Bayan kashe mutane 6 da suka sun ji wa wasu 20 rauni.
Wani mazaunin kauyen Jamilu Hussaini ya ce maharan sun bi mutane har a gonakinsu suka bude musu wuta, sai da kuma tuni an garzaya da wadanda suka samu rauni asibiti a Zariya.
Hussaini ya ce maharan sun far wa kauyen ranar Juma’a da rana sannan suka dawo ranar Asabar a daidai suna suturta wadanda suka rasu.
” Ranar Asabar jiragen yakin sun zo yankin kuma sun yi wa maharan ruwan bama-bamai daga sama. Sun tarwatsa inda suke a boya da su kan su.
Rundunar ‘Yan sandan Kaduna ta tabbatar da aukuwar haka.
Discussion about this post