Mahara sun kashe jami’in kwastam a jihar Jigawa

0

Wani jami’in Kwastam ya rasa ransa bayan wasu mahara sun bude wa jami’an wuta a wani harin kwantar bauna da suka kai musu a Ringim.

An ba da labarin cewa akwai wadanda ke ba maharan bayanan sirri daga kauyen wanda ya sa suka iya afka wa jami’an kwastan din.

Maharan sun kashe jami’i daya sannan sun ji wa daya rauni. Amma kuma sun arce da bindigogin jami’an.

PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda wasu ‘yan bindiga suka shiga har cikin Dutse, babban birnin Jihar Jigawa, su ka yi awon gaba da matar Mataimakin Kwamandan Ƴan Bijilante, Abdullahi Suleiman da kuma dan sa.

Rundunar ‘yan sandan Jigawa ta tabbatar da haka, tare da cewa amma sun ceto dan, saura matar ce ta rage a hannun masu garkuwar.

Mazauna unguwar sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan bindigar sun je har gidan Mataimakin Kwamandan da ke Galamawa, kan titin zuwa filin jirgin saman Dutse, wajen 12 na dare.

Sunan wadda aka yi garkuwar da ita Husna, Mai sjelaru 50 kuma dan na ta Umar, dan shekara tara.

Mazauna wurin sun ce mai yiwuwa dama masu garkuwar na fakon mijin ta, wanda shi ne mataimakin kwamandan ‘yan bijilante a jihar Jigawa.

Share.

game da Author