Ɗaya daga cikin lauyoyin dakataccen Shugaban Riko na Hukumar EFCC Ibrahim Magu, ya jajirce cewa tabbas Mai Shari’a Ayo Salami ya furta a gaban su cewa ya na da-na-sanin shugabancin kwamitin binciken Magu da aka ɗora masa nauyi.
PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa lauyoyin Magu biyu, Zainab Abiola da Tosin Ojaoma, sun yi ikirarin cewa Salami ya yi wannan furucin a ranar da su ke kammala gabatar da kare Magu a gaban kwamitin.
Kwamitin dai ana daukar duk bayanan komai a kyamara, a dukkan zaman da ya ke yi a Fadar Shugaban Kasa.
Bayan buga labarin cewa Salami ya yi da-na-sani, tsohon Cif Jojin Najeriya din ya fitar da takardar karyata lauyoyin, inda ya ce shi bai taba cewa ya yi da-na-sanin shugabancin kwamitin binciken Magu ba.
Ya ce lauyoyin karya su ka kantara masa. Amma dai har yanzu bai yi wata barazanar maka su kotu ba, tin bayan karyatawa da ya yi, makonni biyu da su ka gabata.
“Ba ni da wani dalilin da zai sa a ce wai ina da-na-sanin karbar shugabancin kwamitin binciken Magu da na yi.”
Haka ya bayyana cikin wata takardar da ya fitar ga manema labarai, kuma ya sa mata hannu da kan sa.
“Ban taba lauyoyin biyu ko wani ko wasu su fita kafafen yada labarai su yi magana a madadi na ba. Saboda na san a matsayi na na tsohon Cif Jojin Kotun Daukaka Kara ta Kasa, to zan iya bayyana abin da ke raina a ko’ina. Ba sai na tsaya wakilta wani ya yi magana a madadi na ba.
“Na sha warware kulli ko shari’ar da ta fi wannan tsauri. Saboda haka wannan kage ne da sharri kawai aka yi min domin a bata min suna.”
Sai dai kuma da PREMIUM TIMES ta tuntubi Ojaoma dangane da karyata su da Salami ya yi, sai ya ce tabbas Salami ya yi furucin, domin ya wuce ya kantara wa Salami karya.
“Kai ni fa a shirye na ke na yi rantsuwar kaffarar kwansitushin a kotu (wato affidavit).”
An tambaye shi su wa da su wa ke wurin, yayin da Salami ya yi furucin, sai ya ce akwai su lauyoyin Magu da kuma dukkan mambobin kwamitin binciken Magu, wadanda Salami ne shugaban su.
Ya kara da cewa babban lauyan Magu Wahab Shittu ma ya na wurin a lokacin.
PREMIUM TIMES ta kasa samun Shittu kafin buga wannan labari.
Discussion about this post