Kwamitin Shugaban Kasa ya amince a hukunta ‘yan SARS 33, a biya naira milyan 265 kudin diyyar wadanda su ka kashe

0

Kwamitin Binciken Take Hakkin Jama’a da SARS su ka yi, ya kammala bincike, tare da amincewa a gurfanar da jami’an SARS 33 a hukunta su a kotu.

Sannan kuma kwamitin ya ce a biya diyya ta jimlar naira milyan 265 ga iyalan wadanda SARS su ka kashe ko su ka lahanta wa ‘yan uwa.

Babban Sakataren Hukumar Kare Hakkin Jama’a, Tony Ojukwu ne Shugaban Kwamiti. Ya mika rahoton sa a ranar Talata.

“Kwamitin Binciken Ayyukan Assha na SARS a karkashin shugabancin Babban Sakataren NHRC, Tony Ojukwu, ya bayar da shawarwari, ciki har da barin biyan ta tsabar kudi naira milyan 265 da dubu 754 ga wadanda SARS su ka take wa hakki.” Haka wani sashe na rahoton ya bayyana.

Sauran abin da rahoton ya ce a yi sun hada da gurfanar da jami’an SARS 33. Ana ci gaba da binciken wasu korafe-korafe 57 wadanda su ma wadanda abin ya shafa din duk diyya za a biya su.

Sannan kuma akwai wasu kararraki biyu da ke a gaban kotu wadanda Rundunar ‘Yan Sanda ce aka gurfanar. Kuma ita rundunar za ta bi duk umarni ko hukuncin da kotu din ta zartas.

Kwamitin ya kuma zartas cewa za a buga takardar neman afuwa kan wadansu take hakki har 32 da SARS su ka. Za a nemi afuwar ce a rubuce a buga a jaridu da wasu kafafen isar da sako daban-daban.

Share.

game da Author