Kungiyar Likitoci reshen jihar Abia ta yi barazanar fara yajin aiki

0

Kungiyar likitocin Najeriya NMA reshen jihar Abia ta yi barazanar fara yajin aiki idan har jami’an tsaro suka ci gaba da muzguna musu a fadin jihar.

Shugaban kungiyar Chimezie Okwuonu da sakataren kungiyar Robinson Ugwuanyi ne suka bayyana matsayar ‘yan kungiyar a wani takarda da suka raba was manema labarai a garin Umuahia ranar Juma’a.

Kungiyar ta ce jami’an tsaro na muzguna musu a duk lokacin da suka fito aiki duk da cewa gwamnati tace ma’aikatan lafiya basu cikin rukunin mutanen da aka hana wa walwala a jihar.

“Lalle za mu fara yajin aiki nan da sa’o’i 24 idan jami’an tsaro suka ci gaba da muzguna mana.

“Muna kira ga shugabanin asibitocin jihar da su hada hannu da gwamnati domin ganin sun kawo karshe wannan matsala.

NMA ta ce za ta kafa kwamitin ma’aikatan lafiya domin ganin sun kula da kiwon lafiyar mutanen Koda gwamnati ta yi watsi da barazanar su.

Sannan kungiyar ta ce za ta ci gaba da kula da ‘yan zanga-zangan #EndSars da suka ji rauni a lokacin zanga-zanga.

Share.

game da Author