Ku daina farfasa rumbunar ajiyar magunguna – Kira ga matasa

0

Kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar cutar korona, PTF ya yi kira ga mutanen da matasa su daina fasa dakunan ajiyan magunguna suna awon gaba da su a kasar nan.

Kodinatan kwamitin Sani Aliyu ne ya yi wannan kira ranar Litini a taron da kwamitin ke yi da manema labarai a Abuja.

Aliyu ya yi wannan kira ne saboda akwai magungunan da har yanzu ake amfani da su wajen kawar da cutar korona sannan da kayan abincin da mutane da kungiyoyi kamar su CACOVID tara wa gwamnati domin tallafawa mutanen da basu da shi a kasan.

“Duk wadannan kaya da gwamnati ta tara za ta raba wa gwamnonin kasar nan ne domin tallafa wa mutane a kasar nan.

“A dalilin haka kwamitin PTF ke kira ga mutanen da su daina farfasa dakunan ajiyan kaya irin haka sannan su zama masu kiyaye dokokin kasa.

Share.

game da Author