Kowa ya koma makaranta – Inji gwamnatin Legas

0

Gwamnatin jihar Legas ta umarci Iyaye su tasa keyar ƴaƴansu zuwa makaranta daga ranara Litinin mai zuwa.

Ma’aikatar Ilimin jihar ta sanar da haka a wata takarda da Ma’aikatar ta fitar ranar Alhamis.

Wannan karon gwamnati ta ce kowa da kowa ne zai koma domin aci gaba da karatu kafin Kirsimeti.

Kwamishinan Ilmin jihar Folasade Adefisayo, ta yi kira ga yara da malamai da su zake sosai domin kammala wannan zangon karatu da kuma samun daman cike wuraren da ba a yi ba.

” Muna fatan a samu zaman lafiya da natsuwa a jihar, kada wani abin ya kuma tasowa da zai sa asake rufe makarantun jihar. Da farko dai Korona ce, sai kuma wannan tashin hankali na #EndSARS da ya sa dole muka rufe makarantun jihar.

Share.

game da Author