Kotun Daukaka Kara ta yi fatali da ‘yan sanda 10,000 da ta ce Gwamnatin Buhari ta dauka ‘ba bisa ka’ida’ ba

0

Kotun Daukaka Kara ta soke takardun shaidar daukar ‘yan sanda 10,000 da Sufeto Janar Mohammed Adamu ya yi, a cikin 2019.

Har yau kuma Kotun Daukaka Kara ta haramta Dokar ‘Yan Sanda ta 2020, wadda aka rattaba wa hannu cikin Satumba, saboda wani sashe na dokar ya ci karo da Dokar Tsarin Mulki ta 1999.

Dokar Tsarin Mulki ta 1999 dai ta ce Hukumar Kula da Aikin ‘Yan Sanda (Police Service Commission) ce ke da hakkin daukar sabbin ‘yan sanda aiki.

Amma kuma duk da wannan, sai Shugaba Muhammadu Buhari ya amince wa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Adamu, daukar sabbin ‘yan sanda 10,000 cikin 2019.

Duk da cewa Hukumar Kula da ‘Yan Sanda ta Kasa (PSC) ta nuna rashin amincewar ta, kuma ta nuna ba a yi daidai ba, Sufeto Janar Adamu ya yi kunnen-uwar-shegu da koke-koke da korafe-korafen da PSC da wasu kungiyoyin sa-ido kan dimokradiyya su ka rika yi.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Hukumar Kula da ‘Yan Sanda ta Kasa ta maka Sufeto Janar Adamu kotu, shi da Rundunar ‘Yan Sanda ta Kasa (NPF), ta nemi a haramta sabbin ‘yan sandan da Buhari ya amince Adamu ya dauka, cikin watan Disamba, 2019.

Babbar Kotun Tarayya ta yi fatali da karar, ta ce sabbin ‘yan sandan bisa ka’ida aka dauke su.

Mamakin wannan hukunci da kuma rashin gamsuwa da shi ne ya sa PSC ta daukaka kara zuwa Kotun Daukaka Kara ta Kasa. Ita kuma ta duba, ta ce ‘yan sandan da Adamu ya daukaka haramtattu ne.

Babban Mai Shari’a Inyang Ekwo na Kotun Daukaka Kara ya zartas da hukuncin cewa Hukumar Kula Da ‘Yan Sanda ta Kasa ce a karkashin jagorancin Sufeto Janar ke da hakkim daukar sabbin ‘yan sanda.

Ya ce kuskure ne, haramci ne kuma keta doka ce da Sufeto Janar Adamu ya dauki sabbin ‘yan sanda 10,000 ba tare da hada kai an gudanar da daukar a karkashin Hukumar Kula da ‘Yan Sanda ba.

Shi kuwa Babban Mai Shari’a Emmanuel Akomaye na Kotun Daukaka Karar, da ya ke kara bayani dalla-dalla, cewa ya yi:

“Dokar 1999 ta Aikin Dan Sanda a Sadara ta 3 Sashe 1, Kiran-lamba ta 3, cewa ya yi Hukumar Kula da Aikin Dan Sanda ce ke da hakkin nada ‘yan sanda. Don haka sashen bai ce banda sabbin dauka ko karabiti ba.”

Ya ce don haka babu wata kwaskwarima da Majalisar Tarayya za ta iya yi wa wannan sashe don kawai ana so a ba Sufeto Janar Adamu ikon daukar sabbin ‘yan sanda.

Kakakin Yada Labarai na PSC, Ikechukwu Ani, ya ce nan ba da dadewa ba hukumar za ta fito da bayanin sabon tsarin da za ta yi dangane da daukar sabbin kuratan ‘yan sanda.

Share.

game da Author