Babbar kotu a jihar Kano ta yi watsi da karar da aka shigar a gabanta kan zargin sama da fadi wasu kudade da ake yi wa tsohon Gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau.
An gurfanar da Shekarau, Aminu Wali da Mansur Ahmed a kotu kan tuhumar su da a ke yi na karban Naira miliyan 950 daga cikin dala 115 daga hannun tsohuwar ministan albarkatun man fetur Diezani Maduekelokacin kamfen din 2015.
Alkalin kotun Amina Audi ta yi watsi da karar tana mai cewa hukumar EFCC bata iya bayyana kwararan hujjoji da za su nuna cewa Shekarau ya karbi wadannan kudade ba.
Kakakin hukumar EFCC Idris Nadabo ya ce zai yi magana kan hukuncin da kotun ta yanke bayan ya samu izinin yin haka daga nagaba da shi.
Idan ba a manta ba a watan Mayu 2918 be hukumar EFCC dake Kano ta Kama tshon gwamna Shekarau bisa tuhumar sa da a keyi da karban wasu kudade daga hannun tsohuwar ministan albarkatun man fetur Diezani Madueke da ya kai naira miliyan 950 a lokacin kamfen din 2015.
Kakakin tsohon gwamna Shekarau, Sule, ya karyata dalilan da aka bada wai sune yasa aka tasa keyar mai gidan sa.
Ibrahin Shekarau ya canja sheka zuwa jam’iyyar APC, kuma yayi takarar sanata a 2019. Ya ci zabe.